Da dumi-dumi: Rundunar soji ta kai farmaki sansanin ‘yan bindiga, ta ceto babban sojan da aka sace a NDA

Da dumi-dumi: Rundunar soji ta kai farmaki sansanin ‘yan bindiga, ta ceto babban sojan da aka sace a NDA

  • Babban sojan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi kwanan nan a Kwalejin horar na sojoji na Najeriya ya samu 'yanci
  • An rahoto cewa Manjo CL Datong ya sami 'yanci bayan da sojojin Najeriya suka kai suka wani samame kan 'yan bindigar cikin nasara
  • A yayin aikin ceton, an lalata sansanin 'yan ta'adda da dama a yankunan Afaka- Birnin Gwari

Kaduna - Manjo CL Datong, wanda aka yi garkuwa da shi lokacin da 'yan bindiga suka kutsa cikin Kwalejin horar da sojoji na Najeriya (NDA) a Kaduna, a watan da ya gabata, ya samu ‘yanci, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An kashe manyan jami’an biyu a lamarin wanda ya faru a ranar 24 ga Agusta, 2021.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi na karfafa fashi da makami a arewa, Kungiyar CAN ta yi zargi

Da dumi-dumi: Rundunar soji ta kai farmaki sansanin ‘yan bindiga, ta ceto babban sojan da aka sace a NDA
Da dumi-dumi: Rundunar soji ta kai farmaki sansanin ‘yan bindiga, ta ceto babban sojan da aka sace a NDA Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

A daren Juma'a, 17 ga watan Satumba, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Runduna ta 1, Sojojin Najeriya, Kanal Ezindu Idimah, ya ce sojoji sun ceto Datong, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce ayyukan da suka kai ga kubutar da shi sun kai ga rusa sansanonin ‘yan ta’adda da aka gano a yankunan Afaka- Birnin Gwari na jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma kara da cewa an kashe dimbin 'yan bindiga a yayin farmakin, musamman, a cikin daren 17 ga watan Satumba, 2021.

Ya ce sashin tare da hadin gwiwar Rundunar Sojojin Sama, hukumar tsaro na farin kaya da sauran hukumomin tsaro, sun gaggauta daukar mataki ta hanyar gudanar da ayyuka a yankin Afaka don ganowa da kubutar da jami'in bayan umarnin Babban Hafsan Sojojin.

Wasu ‘Yan bindigan da aka fatattako daga Zamfara sun tare hanyoyin Katsina suna neman abinci

Kara karanta wannan

Janar Faruk Yahaya: Za mu ji da 'yan bindiga da yaren da suke fahimta

A wani labarin kuma, mun ji cewa mazauna wasu kauyukan karamar hukumar Kankara a jihar Katsina sun ankarar da jama’a game da shigo war ‘yan bindiga a yankin.

Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Juma’a, 17 ga watan Satumba, 2021, cewa an ga ‘yan bindigan da sojoji suka koro daga Zamfara a jihar Katsina.

Majiya tace an ga wadannan ‘yan bindiga a cikin zuga suna tsere wa daga kauyukan na garin Kankara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel