Labari Cikin Hotuna: Sojoji Sun Gudanar da Addu'ar Kwana 40 Ga Marigayi COAS Ibrahim Attahiru

Labari Cikin Hotuna: Sojoji Sun Gudanar da Addu'ar Kwana 40 Ga Marigayi COAS Ibrahim Attahiru

  • Bayan kwana 40 da mutuwar tsohon shugaban sojin ƙasa, COAS Attahiru, sojoji sun gudanar da addu'a ta musamman
  • Sojojin sun bayyana cewa tsohon shugabansu da jami'an dake tare da shi zasu cigaba da kasancewa a zuciyoyinsu
  • COAS Farouk Yahaya, yace rundunar soji ba zata taɓa mantawa da waɗannan gwarazan sojin ba

Sojoji sun gudanar da addu'ar 40 ga marigayi COAS, Ibrahim Attahiru, tare da sauran manyan jami'ai 10, waɗanda suka rasa rayukansu sanadiyyar hatsarin jirgi a Kaduna ranar 21 ga watan Mayu, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Dalilin da Yasa Na Gudu, Nnamdi Kanu Yayi Jawabi a Gaban Kotu

Addu'ar ta gudana ne bisa jagorancin daraktan al'amuran addinin musulunci na rundunar sojin ƙasa, Janar Shehu Mustapha.

Mustapha yayi addu'a ga rayukan mamatan su samu salama, kuma ya ƙara ta'aziyya ga iyalansu.

Marigayi COAS Ibrahim Attahiru
Rundunar Soji Ta Gudanar da Addu'ar Kwana 40 Ga Marigayi COAS Ibrahim Attahiru Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yace ya kamata yan Najeriya su riƙa tunawa da cewa kowane rai zai ɗanɗani mutuwa, saboda haƙa akwai buƙatar kowa ya yi rayuwa mai kyau cikin biyayya ga Allah.

Mustapha ya ƙara da cewa an shirya wannan taron ne domin tunawa da marigayi shugaban rundunar soji da kuma sauran jami'an da suka rasu tare da shi.

Sojoji sun yi addu'ar zaman lafiya da samun nasara

Hakanan kuma sojojin sun yi addu'an neman zaman lafiya tsakanin yan Najeriya da kuma nasara ga sojin dake yaki a ɓangarori daban-daban na ƙasar nan.

Mustapha, yace: "Muna amfani da wannan damar domin yin addu'a ga iyalan mamatan, shugabannin tsaron, da kuma zaman lafiya tsakanin yan Najeriya."

"Muna roƙon Allah ya shiga lamarin mu kan wannan ƙalubalen tsaron da ƙasar mu ke fuskanta, idan ma wani laifi muka yi wa Ubangiji, muna rokon ya mana gafara."

"Hakanan muna roƙon Allah ya cigaba da kare shugabannin mu, ya taimake su bisa jagorancin su domin su ceto ƙasar mu daga halin da take ciki."

KARANTA ANAN: Wani Jogon Jam'iyyar PDP Ya Buƙaci INEC Ta Dakatar da Sauya Sheƙar Gwamnoni Zuwa APC

Hotunan wurin taron addu'a

Wurin taron addu'a
Labari Cikin Hotuna: Sojoji Sun Gudanar da Addu'ar Kwana 40 Ga Marigayi COAS Ibrahim Attahiru Hoto: HQNigerianArmy FB fage
Asali: Facebook

Wurin taron addu'a
Labari Cikin Hotuna: Sojoji Sun Gudanar da Addu'ar Kwana 40 Ga Marigayi COAS Ibrahim Attahiru Hoto: HQNigerianArmy FB fage
Asali: Facebook

Hotunan wurin taron addu'a
Labari Cikin Hotuna: Sojoji Sun Gudanar da Addu'ar Kwana 40 Ga Marigayi COAS Ibrahim Attahiru Hoto: HQNigerianArmy FB Fage
Asali: Facebook

Har yanzun muna tuna gwarazan mu da suka mutu

Da yake jawabi a wurin taron, sabon shugaban soji, manjo janar Farouk Yahaya yace wannan abu ne mai kyau yin addu'a ga marigayi COAS da sauran jami'an da suka mutu a hatsarin jirgi.

Yace an shirya wannan taron addu'an ne domin nuna cewa har yanzun mamatan suna cikim zuƙatan sojoji.

"Zamu cigaba da tuna su a cikin zuciyoyin mu, kuma zamu cigaba da yiwa iyalansu fatan alkairi," inji shi.

A wani.labarin kuma Abun Mamaki, Wani Fursuna Ya Yi Digirin Digirgir a Fannin Sadarwa a Gidan Yari

Wani fursuna dake zaman gidan gyaran hali a jihar Anambra ya kammala karatun digirin digirgir, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Jude Onwuzulike, ya karɓi takardun shaidar kammala karatun digirinsa na biyu daga jami'ar NOUN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262