Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Ta Sama da Ƙasa Kan Yan Boko Haram a Dajin Borno

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Ta Sama da Ƙasa Kan Yan Boko Haram a Dajin Borno

  • Gwarazan sojoji sun yi luguden wuta ta sama da ƙasa a maɓoyar yan Boko Haram
  • Rundunar operation haɗin kai da taimakon sojojin sama ne suka jagoranci kai wannan harin a dajin Lambom
  • COAS Farouk Yahaya ya jinjina wa gwarazan sojin tare da taya su murnar samun nasara

Rundunar sojin ƙasa ta bayyana cewa sojojin sashi na 2 na haɗakar jami'an opertion haɗin kai tare da sojojin sama sun kai hari ta sama da ƙasa kan yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a dajin Lambom dake yankin Warktek.

Jami'an sojin sun hallaka yan ta'addan aƙalla 20 a yayin wannan hari da suka ki musu a maɓoyar su, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Duminsa: Sojoji Sun Yi Artabu da Yan Boko Haram Yayin da Suka Kai Hari Sun Hallaka da Dama a Borno

Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Ta Sama da Ƙasa Kan Yan Boko Haram
Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Ta Sama da Ƙasa Kan Yan Boko Haram a Dajin Borno Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A wani jawabi da kakakin rundunar sojin ƙasa, Brig Gen Onyema Nwachukwu, yace:

"Yayin ɗaukar mataki kan sahihin bayanin da aka samu, jami'an sojin ƙasa tare da na sama sun yi luguden wuta kan yan ta'addan, inda suka kutsa can cikin ɗajin Lambom."

"Gwarazan sojin sun yi saurin isa maɓoyan yan ta'addan, suka cigaba da ruwan wuta ta sama da ƙasa, suka kashe aƙalla mutum 20 daga cikin su."

"Sojojin sun samu nasarar ƙwato manyan makaman yaƙi da suka haɗa da bindigar kakkaɓo jirgi, AK-47, motocin yaƙi biyu, sannan kuma suka yi kaca-kaca da wasu motocin yaƙi biyu."

Hafasan sojin ƙasa yayi murna da wannan nasara

A jawabin kakakin sojin ƙasa ya bayyana cewa shugaban rundunar sojin ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya ya nuna farin cikinsa da wannan nasarar da jami'ai suka samu.

Nwachukwu, yace: "COAS Farouk Yahaya ya taya gwarazan sojojin murna bisa samun nasara a wannan operation da suka fita."

"Ya kuma yi kira gare su da su cigaba da irin wannan aikin ƙarƙashin rundunar operation Haɗin Kai, Har sai an ga bayan yan ta'adda baki ɗaya."

KARANTA ANAN: Sace Ɗalibai a Yauri: Sojoji Sun Sake Ragargazan Yan Bindiga Sun Kuɓutar da Malami da Wasu Dalibai

COAS ya ƙara jaddada kudirin rundunar sojin ƙasa, ƙarƙashin jagorancin sa na kawo ƙarshen matsalar tsaro a yakin arewa maso gabas.

A wani labarin kuma El-Rufa'i Ya Yi Kakkausan Gargaɗi Ga Mutanen Dake Toshe Hanyar Kaduna-Abuja

Gwamnan Kaduna , Malam Nasiru El-Rufa'i ya gargaɗi mutanen jihar sa a kan toshe hanyar Kaduna-Abuja, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnan yayi wannan gargaɗi ne yayin ziyarar ta'aziyya da yakai yankunan, inda ya tattauna da mutanen yankunan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262