Da dumi-dumi: Majalisa ta tabbatar da Yahaya Farouk a matsayin COAS

Da dumi-dumi: Majalisa ta tabbatar da Yahaya Farouk a matsayin COAS

  • Majalisar Dattijan Nigeria, NASS, ta tabbatar da Manjo Janar Faruk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojojin kasa
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi Manja Yahaya ne ya maye gurbin magabacinsa Ibrahim Attahiru ya da rasu a hatsarin jirgin sama
  • Majalisar ta amince da nadin Faruk Yahaya ne bayan kwamitin tsaro na majalisar ta tantance shi ta kuma gamsu da nadin

Majalisar dattawar Nigeria, a ranar Talata ta tabbatar da nadin Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojojin kasa na Nigeria, The Punch ta ruwaito.

Vanguard ta ruwaito cewa majalisar ta cimma wannan matsayar ne bayan duba rahoton kwamitin hadaka kan tsaro karkashin jagorancin Sanata Aliyu Wamakko da Ali Ndume.

Da dumi-dumi: Majalisa ta tabbatar da Yahaya Farouk a matsayin COAS
Da dumi-dumi: Majalisa ta tabbatar da Yahaya Farouk a matsayin COAS
Asali: Original

DUBA WANNAN: Sheikh Gumi ya faɗawa gwamnatin tarayya abin da za ta yi don hana satar ɗalibai a makarantu

A ranar 2 ga watan Yuni ne shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa majalisar bukatarsa na neman amincewarsu game da tabbatar da nadin Yahaya.

An dora wa kwamitin tsaron karkashin jagorancin Wamakko nauyin tantance sabon babban hafsan sojojin kasar.

KU KARANTA: Sheikh Gumi ya faɗawa gwamnatin tarayya abin da za ta yi don hana satar ɗalibai a makarantu

Kafin nadin Yahaya, shine babban kwamandan Division 1 na dakarun sojoji da ke yaki da yan ta'adda a yankin kudu maso gabas na Operation Hadin Kai.

Abin da kwamitin majalisa ta ce game da Faruk Yahaya

Shugaban kwamitin majalisar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko (APC, Sokoto North), a yayin jawabinsa ya ce kwamitin ta gamsu da ayyukan da wanda aka zaban ya yi da yadda ya amsa tambayoyinsu a lokacin tantance shi.

A cewar Wamakko, nadin Faruk ya yi dai-dai da sashi na 217 (2abc) na kudin tsarin mulki na 1999 da aka yi wa kwaskwarim da kuma sashi na 18(1) na dokar sojoji, Cap 20 na shekarar 2004.

Ya kuma ce kwamitin bata samu wani korafi ba daga hukumar yan sandan farin kaya, DSS.

A baya, Farouk Yahaya, mukadashin shugaban rundunar sojin kasa ya ce yana da gogewar da zai iya shawo kan matsalar tsaron kasar nan.

Yahaya ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da lamurran tsaro domin tantancewa.

Shugaban sojin ya ce ya halarci yaki da kwantar da tarzoma a Liberia inda ya kara da cewa gogewarsa kadai ta isa ta inganta tsaron kasar nan, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel