Yanzu-Yanzu: Jiragen Yaƙin Tucano 6 Da Najeriya Ta Saya Daga Amurka Sun Iso Nigeria
- Rundunar sojojin saman Nigeria, NAF, ta sanar da isowar jiragen yaki na Super Tucano daga Amurka
- Bashir Magashi, Ministan tsaro; Faruk Yahaya, babban hafsan sojojin kasa; da Oladayo Amao, babban hafsan sojojin sama ne suka karbi jiragen a Kano
- Tun a watan Yuli babban hafsin sojojin sama, Amao, ya ce ana sa ran zuwan jiragen yaki guda 20 kafin karshen 2021
Rundunar sojojin saman Nigeria, NAF, a ranar Alhamis ta karbi rukuni na farko na jiragen sama na yaki kirar A-29 Super Tucano daga kasar Amurka, The Cable ta ruwaito.
Edward Gabkwet, direktan sashin hulda da jama'a da watsa labarai na hedkwatar rundunar sojojin saman Nigeria da ke Abuja ne ya sanar da hakan.
Rahoton na The Cable ya ce kakakin sojojin saman ya ce jiragen sun iso jihar Kano ne misalin karfe 12.34 na rana.
Bashir Magashi, Ministan tsaro; Faruk Yahaya, babban hafsan sojojin kasa; da Oladayo Amao, babban hafsan sojojin sama ne suka karbi jiragen a Kano.
A ranar 15 ga watan Yuli, Gabkwet ya ce jiragen sun baro Amurka amma za su bi ta kasashe biyar kafin su iso Nigeria.
Ya ce:
"Kashin farko na Jiragen yaki na super tukano guda 6 sun baro Amurka a Laraba 14 ga watan Yuli, suna kan hanyar zuwa Nigeria."
"Jiragen shida za su keto ƙasashen biyar da suka haɗa da, Canada, Greenland, Iceland, Spain da Algeria kafin su iso Nigeria a ƙarshen watan Yuli 2021."
"An shirya bikin ƙaddamar da jiragen zuwa cikin kayan aikin rundunar sojin sama a hukumance jim kaɗan bayan isowarsu a watan Agusta 2021, kuma za'a sanar a lokacin da ya dace."
Tun a watan Yuli babban hafsin sojojin sama, Amao, ya ce ana sa ran zuwan jiragen yaki guda 20 kafin karshen 2021
Ya ce baya da wanda suka iso yanzu, wasu karin Super Tucano shida za su iso a Satumba, yayin da CH-3 biyu da CH-4 UCAV hudu za su iso kasar kafin karshen shekarar 2021
Gwamnatin tarayyar Nigeria ta siyo jirage 12
A watan Fabrairun da ya gabata ne, gwamnatin tarayya ta siyo jiragen 'Super Tucano' guda 12 akan kudi $496 miliyan.
A baya, an sha sanar da ranakun isowar kashin farko na jiragen, kafin wannan sanarwar ta yau Alhamis.
Gwamnati na fatan jiragen zasu taimakawa sojoji a yaƙin da suke yi da yan ta'adda a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Asali: Legit.ng