Ku kai yakin har zuwa mafakar makiya, COAS, Janar Yahaya ya umarci sojoji

Ku kai yakin har zuwa mafakar makiya, COAS, Janar Yahaya ya umarci sojoji

  • Babban hafsan sojojin kasa (COAS), Laftana-Janar Faruk Yahaya, ya kammala rangadin kwanaki biyu na sansanin soji a jihar Katsina
  • Kwamandan sojojin ya yi alkawarin cewa sojoji za su kawar da 'yan ta'adda da ke addabar mazauna yankin arewa
  • Yahaya ya ce ana kokarin shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi a kasar a yanzu

Daura, jihar Katsina - Babban hafsan Sojojin kasa (COAS), Faruk Yahaya, ya umarci sojojin Najeriya da su kai yaƙi zuwa maboyar 'yan ta'adda da' yan fashi.

Kwamandan rundunar ya bayar da umarnin a ranar Juma’a, 7 ga watan Agusta, lokacin da yake yi wa sojoji jawabi a sansanin Fort Muhammadu Buhari dake Daura, jihar Katsina.

Ku kai yakin har zuwa mafakar makiya, COAS, Janar Yahaya ya umarci sojoji
COAS Yahaya yayin da yake ziyartan sansanonin soji a fadin kasar Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Yahaya ya bayyana cewa duk da cewar akwai ƙalubale, amma yakamata sojoji su ƙuduri aniyar cin nasarar yaƙin, The Sun ta ruwaito.

Yace:

"Wannan shine abin da muke yi kuma wannan shine abin da za mu ci gaba da yi. Domin duk wurin da na wuce, sakona kenan. Dole ne mu kai yaƙin zuwa wuraren abokan gaba a nan arewa maso yamma har ma a arewa maso gabas inda muke gudanar da su.''

Kara karanta wannan

Ta'addanci: IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta

A cewar Jaridar This Day, Yahaya wanda shi ma ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Daura Umar Farouk Umar, ya nemi goyon bayan sarakunan gargajiya a arewa maso yamma don samun ingantattun bayanai da za su taimaka wa sojoji wajen yakar annobar ta’addanci.

Ya ce wannan muhimmiyar rawa ce da ƙananan hukumomin za su taka kuma yana da mahimmanci wajen yaƙi da ayyukan masu laifi.

IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta

A gefe guda, Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, ya ce an fadada rundunar sojojin Najeriya da yawa, duk da cewar tana da karfin samun nasara a yakin da take yi da masu tayar da kayar baya da 'yan fashi a arewacin kasar.

Jaridar ThisDay ta ruwaito cewa Babangida wanda ake kira IBB ya bayyana hakan a wata hira da aka watsa a ranar Juma'a, 6 ga watan Agusta, a gidan talabijin na Arise.

Kara karanta wannan

2023: Tana shirin kwabewa Tinubu yayin da manyan jiga-jigan PDP da APC suka amince kan wanda zai gaji Buhari

Jigon kasar ya kuma bayyana tsufan kayan aikinsu a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da gurɓacewar yaƙin da ake yi da 'yan fashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel