Ginin Tituna
Gwamnatin Gombe za ta kashe naira biliyan 20 kan gina titi mai tsawon kilomita 18.5 a ciki da wajen kwaryar jihar. Kwamishinan ayyuka na jihar ne ya sanar da haka.
Kungiyoyin ma'aikatan dake aikin gina titunan kasar nan sun fusata biyo bayan rashin jituwa tsakaninsu da gwamnati ya yi sanadiyyar korar mambobinsu 52,000.
Akalla mutane 18 ne su ka mutu a babban titin Port Harcour Enugu da ke yankin Umuahia-Enugu a safiyar yau yayin da su ke jira a shingen 'yan sanda.
Hukumomi a jihar Lagos sun dauki gagarumin aikin tsaftace gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba a yankin Lekki. Ana ganin hakan zai taimaka wajen tsaftace jihar.
A yayin da kamfanin CCECC ya ce ya kammala hada layin dogo daga Lagos har zuwa Kano, ita kuma gwamnatin tarayya ce za a fara jigila kan titin a watan gobe.
Majalisar wakilai ta fara gudanar da bincike kan kwangilar aikin gina babban titin da ya taso daga Legas zuwa Calabar. Majalisar na zargin akwai lauje cikin nadi.
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da ginin titin dan Agundi mai hawa uku domin rage cunkoson ababen hawa. Kamfanin CCG Nigeria Limited ne zai yi aikin kan ₦15bn.
Gwamnatin jihar Kebbi ta bayyana cewa ta gano wasu dake yiwa kokarinta zagon kasa. Gwamna Nasir Idris na jihar ne ya yi zargin a garin Zuru yayin bikin Uhola.
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ja kunnen wani dan kwangila da aka ba aikin gina titi a jihar da ya dawo bakin aiki ko ya fuskanci hukunci mai tsauri.
Ginin Tituna
Samu kari