Jihar Rivers
Yayin da ake ci gaba da rikicin siyasa a jihar Rivers, manyan 'yan Majalisun Tarayya sun nuna goyon bayansu ga Gwamna Fubara na jihar Rivers a yau Juma'a.
Rushe majalisar dokokin jihar Ribas na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ka iya raba Gwamna Fubara da mulki yayin da rigimarsa da Nyesom Wike ke kara kamari.
Kwamishinan ilimi na jihar Rivers, Farfesa Prince Chinedu da kwamishiniyar gidaje, Gift Worlu (PhD) su ne sabbin kwamishinonin da suka yi murabus a ranar Juma'a.
Rikicin siyasar jihar Ribas ya dauki sabon salo tun bayan da gwamna Sim Fubara ya rusa majalisar dokokin jihar, kawo yanzu kwamishinoni takwas sun yi murabus.
Wutar rikici a jihar Rivers ta kara ruruwa yayin da kwamishinoni hudu suka yi murabus a ranar Alhamis. Kwamishinonin na goyon bayan Wike maimakon Gwamna Fubara.
An fara zawarcin Nyesom Wike gadan-gadan a PDP domin mika masa shugabancin APC. Shugabannin jam’iyyar APC na Ribas sun fito a mutum domin a yaki Simi Fubara.
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ta fara nazari kan bin matakan tsige Gwamna Fubara na jihar Ribas daga kan madafun iko kan abiɓda ta kira take doka da oda.
Yayin da rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara da Wike ke ƙara munana, karin kwamishinoni biyu sun yi murabus daga muƙamansu na majalisar zartarwan jihar Ribas.
Yan majalisar dokokin jihar Ribas 26 sun yi zama na musamman a rukunin gidajen yan majalisu kwana ɗaya bayan Gwamna Fubara ya rushe zauren majalisar.
Jihar Rivers
Samu kari