Jihar Oyo
Yayan gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, Injiniya Sunday Makinde ya rasu da daren ranar Juma'a a gidanda da ke Ibadan, iyalai da ƴan uwa sun fara jimami.
Hukumar kwana-kwana ta tabbatar da faɗuwar wata fankar man fetur a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta ce direba ya rasa rayuwansa amma an ceto yaron mota.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwan tsohon shugaban hukumar OYSAA kuma babban jigon PDP, Hon. Temilola Segun Adibi.
Masu zaben sarki a jihar Oyo sun gindaya wa'adin kwanaki 30 ga Gwamna Seyi Makinde ya soke naɗin sabon Alaafin, sun ce ba shi da hurumi a wannan al'amarin.
Popoola Joshua, tsohon ɗan takarar NNPP a Oyo, ya koma APC don ƙarfafa jam’iyyar. Tuni Ganduje ya umarci APC ta yi tsare-tsare domin karɓar mulki daga PDP.
Gwamnatin Oyo karƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde ta lashi takobin tabbatar da tsaron al'umma ko ta wane hali, ta ɗauki matakin hana miyagu sakat.
Hukumar yaki da masu cin hanci da rashawa a Najeriya watau EFCC ta fara titsiye sarakunan da ke zaben sabon Alaafin na Oyo kan zargin karɓar rashawa.
Gwamna Seyi Makinde ya gargadi masu neman ta da rigima bayan an zabi sabon Alaafin na Oyo, Oba Akeem Abimbola Owoade, ta hanyar gaskiya da adalci.
Gwamna Seyi Makinde ya miƙa sandar mulki ga sabon Alaafin na Oyo, Abimbola Akeem Owoade. An mika sandar ne duk da adawa 'yan majalisar nadin sarki ta Oyomesi.
Jihar Oyo
Samu kari