Jihar Osun
Majalisar jihar Osun tayi watsi da bukatar sabon gwamna Sanata Ademola Adeleke na canza sunan jihar. Majalisar tace taken jihar, tambari da tuta duk dokoki ne.
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya fatattaki ma’aikata 12,000 washegarin rantsar da shi sabon zababben Gwamnan jihar. Ya tube rawunan sarakuna 3 na jihar.
Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya yi manyan nade-nade uku awanni bayan rantsar da shi a ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba, sun fara aiki nan take.
Sanata Adeleke Ademola ya tabbata sabon zababben Gwamnan jihar Osun bayan rantsuwar kama aiki da ya karba a yau Lahadi, 27 ga watan Nuwamba wurin karfe 11:54.
Wata kotu da ke zamanta a Osogbo, jihar Osun ta tsige dukkan sabbin shugabannin kanananan hukumomi da kansiloli na jam'iyyar APC kan rashin bin doka yayin zabe.
Gwamna jihar Osun mai barin gado, Adegboyega Oyetola, ya amince da naɗa ma'aikata 30 a matsayin manyan sakatarorin gwamnatina a wata sanarwa da aka fitar .
Hankula sun matukar tashi yayin da rikici ya balle a fadar Ikirun dake jihar Osun bayan an nada sabon sarki wanda ‘yan gidan sarauta suka ce basu so ko kadan.
Jami'an tsaro sun kama wata mota maƙare da bindigogi da wasu mutane zata shiga babbar kotun jihar Osun dake sauraron ƙarar zabe yau Laraba, an gano su waye.
Sarkin Iwo, Oba Abdulrashed Akanbi Telu 1 ya yi kira ga takwarorinsa na kasar Yarbawa su koma ga Allah kuma su daina hada Allah da wani. Sun yi masa martani.
Jihar Osun
Samu kari