COVID-19: Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta kawowa Osun agajin N5bn - Oke
Kawo yanzu an samu mutane fiye da 230 da su ka kamu da cutar Coronavirus a fadin Najeriya. Jihar Osun ta na cikin jihohin da ta ke tsakiyar wannan annoba a kasar.
A dalilin haka ne wani ‘Dan majalisar jihar Osun, Honarabul Oluwole Oke, ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taimakawa jihar Kudancin kasar da agajin kudi.
Oluwole Oke mai wakiltar Obokun da Oriade majalisar wakilan tarayya ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta ba jihar ta sa tallafin Naira biliyan 5 domin yakar Coronavirus.
A wani jawabi da Oluwole Oke ya fitar, ya bayyana cewa akwai bukatar a kawowa Osun dauki ganin cewa an samu mutane 22 da su ka kamu da wannan cuta a cikin jihar.
Sai dai alkaluman hukumar NCDC sun nuna cewa mutane 20 ne su ka kamu da cutar a jihar Osun. Wannan ya na nufin Osun ce ta ke bin bayan Jihar Legas da birnin tarayya.
KU KARANTA: Coronavirus ta dauki sabon salon shiga jikin mutane a Najeriya
Oke wanda shi ne shugaban wani muhimmin kwamiti a majalisar wakilai ya ce akwai bukatar shugaban kasa Buhari ya yi maza ya ceci jihar Osun daga halin da ta shiga.
“Ina tunanin a wannan lokaci, ya kamata shugaban kasa ya sa hannu a matslar da jihar Osun ta ke fuskanta, tun kafin lamarin ya yi kamari ya addabi kasar gaba daya.”
“Ka sani cewa wannan mummunar cuta ba ta san shekaru ba, kuma babu ruwanta da matsayin mutum ko kuma kasar da ya fito ko martabarsa a cikin al’umma.” Inji Oke.
Har yanzu ba mu samu labarin cewa fadar shugaban kasa ta maida martani game da wannan roko na ‘dan majalisa Oluwole Oke wanda ya ke karkashin jam’iyyar PDP.
Tsakanin babban birnin tarayya Abuja zuwa Legas da kuma jihar Osun, akwai mutane kusan 190 da su ka kamu da Coronovirus. Mutane biyar cutar ta kashe a halin yanzu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng