'Yan sanda sun kamo mai cutar covid-19 da ta tsere daga cibiyar killacewa

'Yan sanda sun kamo mai cutar covid-19 da ta tsere daga cibiyar killacewa

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Osun sun sanar da kama mai dauke da kwayar cutar covid-19 bayan ya tsere daga cibiyar killacewa a jihar da ke Ejigbo.

Jami'an 'yan sanda sun kama matar ne ranar Asabar tare da mayar da ita cibiyar killacewar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Osun, Johnson Kokumo, yana cikin cibiyar killacewar a ranar ta Asabar da aka dawo da matar.

Sakataren yada labaran gwamnan jihar Osun, Ismail Omipidan, ya tabbatar da cewa an mayar da mai dauke da kwayar cutar zuwa cibiyar killacewar jihar.

Ya zuwa yanzu an kara tsaurara matakan tsaro a bakin kofar shiga cibiyar. Jaridar Punch ta rawaito cewa an ajiye jami'an 'yan sanda da na DSS a bakin babbar kofar cibiyar kilacewar.

'Yan sanda sun kamo mai cutar covid-19 da ta tsere daga cibiyar killacewa
Cibiyar killacewa
Source: Facebook

An ga kwamishinan 'yan sanda, Kukomo, da kansa yana bawa jami'an tsaro umarni a cibiyar.

A cikin makon da muke bankwana da shine Legit.ng ta wallafa cewa Osagie Ehanire, ministan lafiya, ya ce mutane tara da aka samu suna dauke da kwayar cutar coronavirus a jihar Osun sun shiga Najeriya ne ta barauniyar hanya da ke kan iyakarta da kasar Benin.

DUBA WANNAN: Coronavirus: Gwamnatin Kano ta bude shafin yanar gizo na daukan ma'aikatan lafiya

Da yake ganawa da manema labarai bayan kammala taron kwamitin da shugaban kasa ya kafa annobar covid-19, ministan ya bayyana cewa masu dauke da kwayar cutar sun fito ne daga kasar Kwadebuwa sannan suka bi ta cikin kasar Benin, kafin daga bisani su shigo Najeriya ta wata barauniyar hanya.

Ya ce an yi nasarar datse motar da ta dauko su tare da gudanar da gwaji a kansu. Ya bayyana cewa dukkan mutanen cikin motar, 'yan Najeriya ne da suke son dawowa bayan an rufe iyakokin kasa.

Ya zuwa yanzu akwai masu dauke da kwayar cutar coronavirus guda 14 a jihar Osun, lamarin da ya saka su kasancewa jiha ta uku da ke da yawan masu dauke da kwayar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel