An gano ta barauniyar hanyar da masu cutar coronavirus 9 suka shigo Najeriya

An gano ta barauniyar hanyar da masu cutar coronavirus 9 suka shigo Najeriya

Osagie Ehanire, ministan lafiya, ya ce mutane tara da aka samu suna dauke da kwayar cutar coronavirus a jihar Osun sun shiga Najeriya ne ta barauniyar hanya da ke kan iyakarta da kasar Benin.

Da yake ganawa da manema labarai bayan kammala taron kwamitin da shugaban kasa ya kafa annobar covid-19, ministan ya bayyana cewa masu dauke da kwayar cutar sun fito ne daga kasar Kwadebuwa sannan suka bi ta cikin kasar Benin, kafin daga bisani su shigo Najeriya ta wata barauniyar hanya.

Ya ce an yi nasarar datse motar da ta dauko su tare da gudanar da gwaji a kansu. Ya bayyana cewa dukkan mutanen cikin motar, 'yan Najeriya ne da suke son dawowa bayan an rufe iyakokin kasa.

Ya zuwa yanzu akwai masu dauke da kwayar cutar coronavirus guda 14 a jihar Osun, lamarin da ya saka su kasancewa jiha ta uku da ke da yawan masu dauke da kwayar cutar.

An gano ta barauniyar hanyar da masu cutar coronavirus 9 suka shigo Najeriya
Gboyega Oyetola, gwamnan jihar Osun.
Asali: Facebook

A jerin wasu sakonni da gwamnatin jihar ta fitar a shafin tuwita domin kwantar da hankalin jama'a, ta bayyana cewa, "mun san ba labari bane mai dadi cewar an samu mutane 14 da ke dauke da kwayar cutar coronavirus, amma labari mai dadi shine; gwamnati tana yin iya bakin kokarinta domin dakile yaduwar cutar tare da tabbatar da ganin cewa masu dauke da ita sun warke."

DUBA WANNAN: Covid-19: Wata yarinya mai shekaru 8 ta rubutawa Buhari wasika, ta bayar da tallafin N2,350

A ranar Lahadi ne gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta saka dokar rufe shige da fice tare da taron jama'a don dakile yaduwar annobar covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel