Garkuwa da mutane, fashi, ba su san wani addini ba – Oyetola ga MURIC

Garkuwa da mutane, fashi, ba su san wani addini ba – Oyetola ga MURIC

Gwamna Adegboyega Oyetola na Osun, ya yi kira ga duk wanda ya ke jiharsa da ya marawa Jami’an Amotekun da aka kirkira a Kudancin kasar baya.

Adegboyega Oyetola ya maida martani ne ga kungiyar MURIC wanda ta ke zargin cewa ana kokarin maida Dakarun wasu Sojojin kiristoci a Najeriya.

Mai girma gwamnan ya yi wannan jawabi ne ta bakin babban Sakatarensa na yada labarai, Ismail Omipidan a Yau Ranar Laraba, 22 ga Watan Junairun 2020.

Omipidan ya ke mamakin ko laifufffuka irinsu fyade, garkuwa da mutane, da ta’adi da makami sun san addini, inda ya kare wannan shiri da aka kawo.

“Amotekun yunkurin kai-da-kai ne da Kudu maso Yammacin Najeriya su ka yi na kawo karshen ta’adi, fyade, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka."

KU KARANTA: Asirin wani kwarto da ke shigar mata ya tonu a Najeriya

“Don haka a rika tunanin cewa wannan shiri ya na da burbushin addini ko kusanci da wani addini, mummunan abu ne wanda ka iya jawo bakin-jini."

Oyetola ya jaddada cewa sun dogara ne da sashe na 14 (2) (b) na kundin tsarin mulkin Najeriya wajen kirkiro wadannan Dakarun tsaro na Amotekun.

A cewarsa, ya zama dole gwamnatin jiha ko da tarayya ta yi duk abin da za ta iya wajen ganin ta tsare rayukan jama’a da dukiyoyinsu a fadin Najeriya.

“A maimakon mu rika adawa da wannan shiri da mu ka yi ta kukan a kawo domin takaita barazanar da ta sa aka soki wasu gwamnoni, mu hadu mu marawa Amotekun baya ta kawo dabaru domin ayi aiki da juna tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnonin Kudu na yamma.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel