Sarki ya yi wa wani basarake dukan tsiya a Osun

Sarki ya yi wa wani basarake dukan tsiya a Osun

A ranar Juma’a ne aka zargi mai martaba Oluwo na Iwo, Abdulrosheed Akanbi da dukan wani basarake mai suna Dhikrullah Akinropo wanda shine Agbowu na Ogbaagba a kan matsalar fili. An yi hakan ne a ofishin mataimakin sifeta janar din ‘yan sanda da ke Zone 11 a Osogbo.

Jaridar Premium Times ta gano cewa lamarin ya faru ne a yayin da ake yin taron wanzar da zaman lafiya wanda mataimakin sifeta janar, Bashir Makama ya shirya sakamakon rikicin da ake kan filaye a Iwo.

Majiya da daga sun tabbatar da cewa tun kafin nan, Akanbi ya umarci sauran masu sarautar da su daina siyar da filayen ba tare da saninsa ba.

Jaridar Premium Times ta gano cewa bayan anyi taruka da dama don kawo karshen rashin jituwar kuma dole ta sa ‘yan sanda suka shiga lamarin.

Sauran masu sarautar da suka halarci taron na ranar Juma’a din sun hada da Quadri Adeoye, Oluwo na Iwo-Oke; Oyebamiji Oyeleso na Oluponna, Adio Oyediran na yankin Igege, Solomon Ojo na Ikonifin, Moshood Oparonke na Eesu, da sauransu.

Sarki ya yi wa wani basarake dukan tsiya a Osun
Sarki ya yi wa wani basarake dukan tsiya a Osun
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mutane 10 da suka fi kowa arziki a Najeriya a 2020 da kiyasin dukiyarsu (Hotuna)

A yayin da ake taron, Akanbi ya yi tattaki har zuwa inda Akinropo ke tsaye sannan ya fara dukan shi.

Ganau ba jiyau ba da ya zanta da Premium Times amma ya bukaci a boye sunansa, ya ce sai da mataimakin sifeta janar din ya taimaka sannan ya dena dukan Akinropo.

A take kuwa aka gaggauta garzayawa da Akinropo zuwa asibiti da ke Osogbo don duba lafiyarsa sakamakon farfasa masa baki da yayi.

Duk da rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun ki cewa komai a kan harin, amma wani mai sararutar gargajiya ya bayyana abinda ya kai su asibitin.

A yayin da Akanbi bai musanta dukan basaraken ba, ya ce ya kare kansa ne saboda Akinropo yayi kokarin dukan wani hadiminsa a kan idonsa.

Kamar yadda fadar sarakunan biyu suka bayyana, sun tabbatar da aukuwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel