Coronavirus: Sanatan Najeriya ya killace kansa bayan dawowa daga Ingila
- Sanatan Najeriya mai wakiltar jihar Osun ta tsakiya, Sanata Ajibola Basiru ya killace kansa bayan tafiyar da ya dawo daga Ingila
- Basiru ya sanar da hakan ne yayin martani ga wasikar Abba Kyari, a inda yake zarginsu da kin bin ka'idojin gujewa yaduwar muguwar cutar
- A martanin Bashir ya ce bai halarci kowanne taro ba tun bayan da ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa Ingila
Sanatan Najeriya mai wakiltar jihar Osun ta tsakiya, Sanata Ajibola Basiru ya killace kansa bayan tafiyar da ya dawo daga Ingila, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Basiru ya sanar da hakan ne yayin martani ga wasikar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, a inda yake zargin cewa wasu daga cikin 'yan majalisar tarayyar da suka dawo daga tafiya kasashen ketare sun ki bin ka'idojin gujewa yaduwar muguwar cutar coronavirus.
A wasikar, Kyari ya zargi wasu daga cikin 'yan majalisar da laifin kin bin ka'idojin tantancewa a filayen jiragen saman Najeriya.
Wasikar ta bazu a yanar gizo a ranar Litinin dauke da kwanan wata 21 ga watan Maris, wacce aka saka adireshin kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Abba Kyari: Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya kamu da Coronavirus
A martanin Bashir, wanda shine shugaban kwamitin majalisar dattijai a kan 'yan Najeriya mazauna waje, ya ce bai halarci kowanne taro ba tun bayan da ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa Ingila.
Ya wallafa a shafinsa na twitter, "Ba kamar yadda rahoto ke nunawa ba cewa sanatocin da suka yi tafiya zuwa Ingila a kan al'amarin iskar gas da man fetur sun ki bin ka'idojin gujewa yaduwar COVID-19 , na killace kaina tun bayan dawowata."
"A don haka ne yasa ban je majalisar dattijan ba kuma ban halarci wani taron kasuwanci ko wani abu ba. Hakazalika NCDC sun tuntubi magaji na don jin cewa ko ina lafiya. A halin yanzu ina lafiya a gida kuma ina morar hutuna." ya kara da cewa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng