Yanzu Yanzu: An samu bullar coronavirus karo na farko a jahar Osun

Yanzu Yanzu: An samu bullar coronavirus karo na farko a jahar Osun

- Gwamna Gboyega Oyetola ya ce shi da matarsa sun yi gwajin coronavirus saboda ziyarar da ya kai Abuja kwanan nan

- Gwamnan ya kuma bayar da tabbacin cewa ana nan ana yiwa tufkar hanci bayan an tabbatar da bullar cutar karo na farko a jahar

- Oyetola ya bukaci dukkanin mutanen da suka dawo daga Ingila, Amurka da sauran kasashen waje da su killace kansu sannan su je su yi gwajin

Gwamna Gboyega Oyetola ya yi kira ga a kwantar da hankali biyo bayan tabbatar da bullar cutar coronavirus karo na farko da cibiyar hana yaduwa cututtuka na Najeriya ta yi a jahar Osun.

NCDC a safiyar ranar Laraba, 25 ga watan Maris ta tabbatar da sabbin mutane biyu da suka kamu a Najeriya. Hukumar a shafinta na twitter ta bayyana cewa mutum daya daga jahar Osun ne yayinda dayan ya fito daga Lagas.

Da ya ke jawabi ga mutanen jahar biyo bayan tabbatar da lamarin da NCDC ta yi, Oyetola ya ce wani da ya dawo daga Ingila ne ya kamu kuma yana samun kulawar likita a yanzu.

Gwamnan ya ce gwamnati ta shirya abun hawa domin kwaso iyalan mutumin da kuma fara neman wadanda suka yi hulda da mutumin da aka samu da cutar.

Gwamna Oyetola ya bukaci dukkanin mutanen da suka dawo daga Ingila, Amurka da sauran kasashen waje da su killace kansu sannan su je su yi gwajin.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Gwamna Obaseki ya shiga killace kansa

Ya ce hakan zai taimaka wajen hana yaduwar cutar a jahar Osun.

A bangare guda mun ji cewa Ministan babbar birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, ya ce za a mayar a babbar asibitin Zuba zuwa cibiyar killace mutane duk a matakan da ake dauka na hana yaduwar cutar coronavirus a Abuja.

Da yake jawabi ga manema labarai, Bello ya ce yana aiki tare da asibitin koyarwa na jami’ar Abuja domin bunkasa cibiyar killace masu dauke da cutar na Gwagwalada.

Ya jadadda cewar har yanzu akwai dokar hana taron jama’a da suka tasar ma mutane 50; yayinda ya kaddamar da rufe harkoki kadan a birnin tarayyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel