Sabbin mutum 5 sun kamu da coronavirus, ta shiga karin sabbin jihohi 2

Sabbin mutum 5 sun kamu da coronavirus, ta shiga karin sabbin jihohi 2

An samu karin sabbin mutane biyar sun kamu da kwayar cutar coronavirus a Najeriya: biyu a jihar Legas, biyu a Abuja, da kuma mutum daya daga jihar Ribas.

A sanarwar da ta fitar a shafinta na tuwita da daren ranar Laraba, cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa uku daga cikin mutanen matafiya da suka dawo Najeriya yayin da mutane biyu sun kamu da kwayar cutar ne sakamakon cudanya da masu dauke da kwayar cutar.

Ya zuwa yanzu jimillar masu dauke da kwayar cutar a Najeriya ya koma mutum 51 a jihohin Najeriya 9.

Hakan ya nuna cewa kwayar cutar coronavirus ta shiga jihohin Osun da Ribas a karon farko.

Ya zuwa yanzu kwayar cutar coronavirus ta hallaka mutane 15,000 a fadin duniya.

Mutum daya ne ya mutu a Najeriya bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus, sannan an sallami mutane biyu da suka warke bayan sun sha magungun a cibiyar da aka killace su, kamar yadda kididdigar NCDC ta nuna.

Yawacin mutanen da aka samu da kwayar cutar corona a Najeriya, 'yan kasa ne da suka dawo daga kasashen ketare, musamman turai.

An tabbatar da samun kwayar cutar a jikin manyan jami'an gwamnati guda uku.

DUBA WANNAN: COVID-19: An haramtawa adaidaita sahu daukar fasinjoji, an saka wa masu mota sabuwar doka a Kaduna

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, shine na farko da aka fara tabbatarwa yana dauke da kwayar cutar. Na biyu shine gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, sai kuma kakakin majalisar jihar Edo.

Ya zuwa yanzu, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da wasu gwamnoni da manyan jami'an gwamnati sun killace kansu bayan sun gano cewa sun yi mu'amala da masu dauke da kwayar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng