An gano coci da ake daukar yara kanana ana koya musu karuwanci a jihar Osun

An gano coci da ake daukar yara kanana ana koya musu karuwanci a jihar Osun

- Wani rahoto ya bayyana cewa wata mata babbar Fasto an kamata da laifin hada yara kanana da maza don karuwanci

- Bayan damketa da rundunar ‘yan sandan jihar Ondo tayi, ta ce ana bata N600 ne a matsayin ladar hada mazan da yaran kanana

- Kamar yadda daya daga cikin yaran ta sanar, shekarunsu basu wuce 13 zuwa 17 kuma duk iyayensu basu tare da juna ne

Wani rahoto da P.M. Express ya ruwaito ya bayyana cewa jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun bankado wani coci na Cherubim da Seraphim, inda fasto mace ke saka kananan ‘yan mata harkar karuwanci.

Rahoton ya bayyana cewa, lamarin na faruwa ne a cocin da ke lamba 37 titin Oriola, a yankin Aladelola da ke jihar Osun.

Fasto Kafayat Idowu mai shekaru 56 ce ta shiga hannun ‘yan sandan sakamakon zarginta da ake da kasuwanci amma na karuwanci a cikin cocinta.

An gano cewa, ‘yan sandan sun samu rahotannin sirri ne a kan lamurran da ke faruwa a cocin ta yadda take saka yara masu karancin shekaru karuwanci. Yaran mata na da shekaru daga 13 zuwa 17 ne kuma tana hada su da kwastomominta.

KU KARANTA: Barawo ya sha ashariya a wajen 'yan sanda bayan ya arce da jakar kudin da suka tara na cin hanci

‘Yan sandan sun dinga bibiyar lamurranta inda daga baya suka kamata tana ciniki da daya daga cikin kwastomomin a cikin cocin Cherubim da Seraphim din. Daga baya da kanta ta sanar da ‘yan sandan cewa tana karbar N600 ne daga kwastomomin don hada su da kananan ‘yan matan.

Daya daga cikin wadanda abin ya faru dasu ce ta sanar da cewa, da yawa daga cikinsu na da shekaru 13 ne zuwa 17 kuma da yawansu iyayensu basu zama tare. Ta kara da cewa an ja hankalinsu ne zuwa karuwanci a lokacin da suka samu Fasto Kafayat don neman taimako.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmed Iliyasu, ya ce wacce ake zargin za a mikata gaban kotu da laifin cin zarafin yara kanana da kuma safarar mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng