Rai ba a bakin komi ba: Yan fashi da makami sun bindige matashi dan bautan kasa

Rai ba a bakin komi ba: Yan fashi da makami sun bindige matashi dan bautan kasa

Wani matashi dan bautan kasa, NYSC, Adebayo Munkaila ya gamu da ajalinsa a hannun wasu miyagun mutane dake fashi da makami bayan sun bindige shi a gaban shagonsa a garin Osogbo na jahar Osun.

Daily Trust ta ruwaito shugaban NYSC na jahar Osun, Adegoke Ayodele ne ya bayyana haka yayin da yake tabbatar da labari ga manema labaru a ranar Laraba, 29 ga watan Janairu, inda yace lamarin ya tayar musu da hankali.

KU KARANTA: Maganganu 4 masu muhimmanci da Sarki Sunusi ya fada ma Gwamna Ganduje

A cewar Mista Adegoke Adewale: “Jim kadan bayan na samu labarin abin da ya faru, sai na sanar da Yansanda, da hukumar NYSC, inda muka yi gaggawar garzayawa da shi domin a binciki gawar, tare da yi masa jana’iza.”

Rahotanni sun bayyana cewa yan fashin sun kashe Munkaila ne a lokacin da suka tare shi da misalin karfe 11 na dare a gaban shagonsa inda yake sayar da katin waya dake kusa da sakatariyar hukumar NYSC a titin Omo-West.

wasu mazauna yankin sun bayyana cewa yan fashin sun tare Munkaila ne a lokacin daya kulle shagonsa zai koma gida, inda yan bindigan suka dirka masa bindiga, sa’annan suka kwashe katukan waya da kuma yan kudaden dake jikinsa.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Buhari ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin manyan iyayen kasa da suka fito daga jahar Neja wadanda suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Gwamba Abubakar Sani Bello.

Sai dai ya gargadi yan bindigan da suka sanya yan Najeriya cikin halin bakin ciki da damuwa, inda yace su jira matakin da gwamnatinsa za ta dauka a kansu, kuma sai sun yi kuka da kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel