Baki shi ke yanka wuya: Rubutu a Facebook ya jefa wani mutumi gidan yari

Baki shi ke yanka wuya: Rubutu a Facebook ya jefa wani mutumi gidan yari

Wata kotun majistri a garin Osogbo na jahar Osun ta tura wani mutumi Akinloye Saheed zuwa gidan kaso biyo bayan wani rubutun karya da yayi a kan Coronavirus a shafin Facebook.

Daily Trust ta ruwaito Yansanda sun kama Saheed ne biyo bayan rubutun da yayi na cewa wai gwamnatin jahar Osun ta shigo da masu cutar COVID-19 zuwa jahar ne da gangan.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Dan bautan kasa ya kamu da cutar Coronavirus a Ondo

Saheed ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar 11 ga watan Afrilu ya ce gwamnatin Osun ta shigo da masu cutar ne domin ta samu tallafin kudi daga wajen gwamnatin tarayya.

Dansanda mai kara, John Idoko ya shaida ma kotu Saheed ya yi rubutun ne da nufin tunzura jama’a su yi ma gwamnatin jahar bore.

Baki shi ke yanka wuya: Rubutu a Facebook ya jefa wani mutumi gidan yari
Baki shi ke yanka wuya: Rubutu a Facebook ya jefa wani mutumi gidan yari
Asali: Facebook

Ya kara da tabbatar ma kotun cewa gwamnatin na kokari domin kuwa zuwa yanzu mutane 10 cikin 17 dake dauke da cutar a jahar sun warke, kuma an sallame su.

Dansandan ya karanta ma kotun rubutun da Saheed ya yi kamar haka: “Lokacin da na zargi gwamnatin Osun da shigo da masu cutar COVID-19 don gwamnatin tarayya ta basu kudi, da dama basu yarda da ni ba.

"sai kuma ya zamana mutanen basu da cutar, APC kun ji kunya.”inji shi.

Laifin da ake tuhumar Saheed ya saba ma dokokin yaki da COVID-19 na jahar Osun na shekarar 2020, hukuncinsa na sashi na 61 na kundin hukunta laifuka na jahar Osun.

Daga nan kuma sai lauyan gwamnatin jahar, Dapo Adeniji ya shaida ma kotu cewa gwamnati na sha’awar shari’ar, don haka za ta dauki ragamar cigaba da karar da aka shigar da Saheed.

Lauya Dapo na karbar ragamar karar ya nemi kotu ta yi watsi da bukatar bayar da belin Saheed kamar yadda lauyansa Bamidele Ajibade ya bukata, wanda hakan ya janyo cecekuce a kotu.

Daga nan sai Alkalin kotun Olusegun Ayilara ya dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Mayu, sa’annan ya bada umarnin a garkame masa Saheed a kurkuku.

A hannu guda, Alkalumma sun tabbatar da cutar Coronavirus ta kashe fiye da mutane 120,000 daga Disambar 2019 zuwa karfe 12 na ranar Talata, 14 ga watan Afrilun 2020.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng