Korona: FG ta gargadi 'yan Najeriya, ta umarci jihohi su samar da karin cibiyoyin killacewa

Korona: FG ta gargadi 'yan Najeriya, ta umarci jihohi su samar da karin cibiyoyin killacewa

A ranar Laraba ne gwamnatin tarayya (FG) ta sake nuna damuwarta a kan halayyar 'yan Najeriya ta yin burus da matakan kare kai da dakile yaduwar annobar cutar korona, musamman a jihohin da aka sassauta dokar kulle.

Wannan shine karo na biyu da FG ta bayyana damuwarta tare da yin gargadi tun bayan sassauta dokar kulle jihohin Abuja, Legas da Osun.

Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban kasa a kan yaki da annobar covid-19, ne ya bayyana rashin jin dadin FG yayin taro da manema labarai a Abuja.

A cewarsa, jama'a, musamman a Abuja da Legas sun yi watsi gaba daya da dukkan dokokin da aka bukaci su yi wa biyayya kafin sassauta dokar kulle jihohin.

Ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nuna damuwarsa a kan karuwar ma'aikatan lafiya da ke kamuwa da kwayar cutar ta korona.

Kazalika, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bawa gwamnatin jihohi umarnin kara yawan cibiyoyin killacewa saboda hauhawar yawan ma su kamuwa da kwayar cutar a kasa.

Tun a ranar Litinin kwamitin PTF ya yi gargadin cewa FG za ta kara garkame jihohin da ta sassauta dokar kulle matukar aka cigaba da samun cunkuson jama'a a kasuwanni, bankuna da ababen hawa na haya.

Korona: FG ta gargadi 'yan Najeriya, ta umarci jihohi su samar da karin cibiyoyin killacewa
Boss Mustapha
Asali: UGC

Kwamitin ya yi gargadi a kan ajiye ma su dauke da kwayar cutar korona da su ke da koshin lafiya a cibiyar killacewa.

Jagoran PTF, Dakta Sani Aliyu, ya shawarci gwamnatocin jihohi a kan kwantar da duk wani mai dauke da kwayar cutar korona, inda ya bayyana cewa zai fi dacewa a jiye kaso 80 na ma su dauke da cutar a wurare ma su kyau kamar Otal.

DUBA WANNAN: An bawa hammata iska a kan gawar mahaifiyar Buratai

Dakta Aliyu ya bayar da wannan shawara ne ranar Laraba yayin taron da kwamitin PTF ya saba gudanarwa da manema labarai a kowacce rana.

Kazalika, ya shawarci jihohi su fara shiri na musamman a cibiyoyinsu na killacewa tare da samar da gadajen kwanciya da yawansu kar ya gaza 300.

Ya bayyana cewa ma su dauke da kwayar cutar da ba su galabaita ko nuna wasu alamun tsananin rashin lafiya ba, ba sa bukatar dawainiya mai yawa, kawai sa mu su ido za a yi da saka mu su wasu ka'idoji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel