Bola Tinubu ne mutumin ya sa na zama kwararren Shugaba – Inji Rauf Aregbesola
- A Ranar 25 ga watan Mayu ne Rauf Aregbesola ya cika shekaru 63 da haihuwa
- A wajen bikin taya Ministan murna, ya yabawa wasu ‘Yan siyasan kasar biyu
- Aregbesola ya fadi yadda Shugaba Buhari da Bola Tinubu su ka taimaka masa
A makon da ya gabata ne ministan harkokin cikin gidan Najeriya watau Ogbeni Rauf Aregbesola ya yi bikin kara shekara da haihuwa, inda ya yi bikin murnar cika shekaru 63 a Duniya.
Rauf Aregbesola ya shirya biki na tunawa da wannan rana mai muhimmanci a rayuwarsa, inda ya ambaci sunan wasu manyan ‘yan siyasa biyu da su ka ba shi gudumuwa a rayuwarsa.
Mai girma Rauf Aregbesola ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma tsohon gwamna Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun taimaka masa sosai a harkar siyasa.
“Tun farko Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance ya na bani goyon baya, sannan ya na karfafa mani, tare da tunzurani domin ganin na taimaki talaka.” Inji Rauf Aregbesola.
KU KARANTA: 'Yan adawa sun rantse sai sun ga baya na - Gwamna Bala
Ministan na harkokin gidan kasa ya kara da cewa a cikin fara’a: “Duk da haka, ba tare da na yi wasa da hakkin sauran tsirarrun mutanen cikin al’umma ba, wanda wannan shi ne jigo.”
A game da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ya fara jawo ministan a jika, ya kira shi kashin-bayansa, wanda shi ne silar duk wata nasara da ya samu a lokacin da ya yi mulki a Osun.
Ogbeni Aregbesola ya ke cewa: “Duk abin da na yi a jihar Osun, sanadiyyar Bola Tinubu ne. Ba zan taba mantawa da irin taimakon da ya yi wajen ganin na zama shugaba na kwarai ba.”
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa bayan Ubangiji, Bola Tinubu ne wanda ya dafawa tafiyarsa. Ministan ya wallafa wannan bayani da ya yi a bidiyo a shafinsa na Tuwita ranar Asabar.
An shirya wannan biki na taya ministan kasar murnar cika shekaru 63 ne ta kafar yanar gizo. Daga cikin wadanda su ka taya ‘dan siyasar murna har da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng