'Yan sanda sun damke wata mata da sassan jikin mutum

'Yan sanda sun damke wata mata da sassan jikin mutum

Rundunar 'yan sandan jihar Osun a ranar Litinin ta damke wata mata da hannayen mutum a garin Ikire. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Osun, Mrs Folashade Odoro ta tabbatar da kamen.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Odoro ta ce wacce ake zargin ta boye hannayen ne a cikin jaka kuma an kama ta ne bayan rahoton sirri da rundunar ta samu.

Kakakin rundunar 'yan sandan ta ce, Kwamishinan 'yan sandan jihar Johnson Kokumo ya ba 'yan sanda umarnin tabbatar da ingantaccen bincike a kan lamarin.

Kokumo ya ce matar ta aikata babban laifi na samunta da aka yi da sassan jikin dan Adam kuma duk wanda aka kama da irin wannan laifin dole ne ya fuskanci fushin hukuma.

'Yan sanda sun damke wata mata da sassan jikin mutum
'Yan sanda sun damke wata mata da sassan jikin mutum
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta bayyana kasar da ta hana Najeriya zama lafiya

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Borno ta tabbatar da kama wani matashi mai shekaru 21 bisa zarginsa da satar litattafai fiye da 100 a masallatai da ke Maiduguri.

Matashin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an kama shi ne yayin da yako kokarin sake tafka wata satar a wani masallacin.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Borno, Mohammed Aliyu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa jama'a ne suka kama matashin ranar 7 ga watan Fabrairu.

A cewar kwamishinan, binciken rundunar 'yan sanda ya nuna cewa an taba samun matashin da laifin sace wasu litattafan addini 100 kafin a kama shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel