Jihar Ondo
Wasu da ake zargin 'yan daba ne a zaga-zagar Edsars sun kona ofishin 'yan sanda da ke karamar hukumar Ifelodun na jihar Legas, a yau Talata, 20 ga wata Oktoba.
Jam'iyyar APC wacce ta sake lashe zaben gwamna jihar Ondo karo na biyu, ta kori mace daya da take da ita a majalisar dokokin jihar saboda zarginta da cin amana.
A zaben bana, Gwamna Rotimi Akeredolu ya kuma doke Eyitayo Jegede. Akeredolu ya doke Jegede karo na biyu, ya nunawa Mataimakinsa Ajayi su ba sa’o’i ba ne.
Gwamnan jihar Ondo, Gwamna Rotimi Akeredolu tare da Lucky Aiyedatiwa, mataimakinsa, sun zagaya titunan Owo domin shagalin bikin murnar nasara da suka samu.
Rotimi Akeredolu ya yi nassarar lasshe zaben gwamnoni na jihar Ondo. Akeredolu na jam'iyyar APC ya samu nassarar samun kuri'u 292,839 yayin da ya lallasa PDP.
Dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ba abokan hamayyarsa a zaben gwamnan jihar Ondo tazara sosai.
Eyitayo Jegede, dan takarar gwamnan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Ondo ya samu gagarumin nasara a kananan hukumomi 2 na Akure.
Dan takarar na jam'iyyar APC ya yi nasarar lashe zaben a kananan hukumomi 9 daga cikin 12 yayin da babban abokin hamayyarsa ya samu nasara a kananan hukumomi 3.
Burin Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo na tazarce yana cigaba da karfi a yayin da aka sanar da sakamakon zabe a kananan hukumomi 12 daga cikin 18 na jihar.
Jihar Ondo
Samu kari