Majalisar dokokin Ondo ta tsige mataimakin kakakinta Iroju Ogundeji

Majalisar dokokin Ondo ta tsige mataimakin kakakinta Iroju Ogundeji

- Rikicin siyasa a majalisar dokokin jihar Ondo ya yi sanadiyar tsige mataimakin kakakin majalisa, Iroju Ogundeji

- An cire Ogundeji daga matsayin a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, a yayin zaman majalisar

- A nan take kuma majalisar ta zabi Samuel Aderoboye a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar

An tsige mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, Iroju Ogundeji, a yayin zaman majalisa na yau Talata, 24 ga watan Nuwamba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsige Ogundeji ya biyo bayan rikicin siyasa da ya addabi majalisar jihar ta kudu maso yamma.

Legit.ng ta tattaro cewa mambobin majalisar dokokin sun kuma zabi Samuel Aderoboye daga mazabar Odigbo a nan take domin maye gurbin mataimakin kakakin majalisar.

Majalisar dokokin Ondo ta tsige mataimakin kakakinta Iroju Ogundeji
Majalisar dokokin Ondo ta tsige mataimakin kakakinta Iroju Ogundeji Hoto: @OndoAssembly
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Dattijo ya roƙi kotu ta ƙwato masa N50,000 daga iyayen budurwar da aka hana shi auren ta

A tuna cewa shugaban majalisar ya dakatar da Ogundeji a baya tare da wani dan majalisa, Adewale Williams.

Dukkanin yan majalisar biyu sun kasance daga cikin yan majalisa tara da suka yi adawa da yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar, Agboola Ajayi.

Ajayi wanda ya bar PDP zuwa jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) ya kara da gwamna mai ci, Rotimi Akeredolu wajen neman kujerar gwamnan jihar.

KU KARANTA KUMA: Hariji kuma matsafi: Kotu ta raba auren mijin da ke saduwa da matarsa tsawon awanni

A gefe guda, mambobi sun tsige kakakin majalisar dokokin jihar Gombe, Abubakar Ibrahim Kurba, tare da shugaban masu rinjaye a majalisar, Samuel Markus Markwina.

Tsohon mataimakin kakakin, Shuaibu Adamu, wanda aka tsige shekarar nan ne ya gabatar da bukatar tsige Kakakin.

Shuaibu Adamu ya karanto takardar tsige Kakakin bayan mambobi 16 cikin 24 sun rattafa hannu.

An alanta Abubakar Muhammad Luggerewo, mai wakiltar mazabar Akko ta tsakiya, matsayin sabon Kakakin Majalisar, yayinda aka sanar da Yarima Gaule mai wakiltar Kaltungo ta gabas matsayin sabon shugaban masu rinjaye.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng