An yi garkuwa da matar shugaban ma'aikatan fadar gwamnan Ondo

An yi garkuwa da matar shugaban ma'aikatan fadar gwamnan Ondo

- Anyi garkuwa da matar shugaban ma'aikatan gwamnar jihar Ondo a daren Alhamis awanni 24 bayan hallaka wani mai sarautar gargajiya a jihar da masu garkuwa da mutane suka yi

- An sanarwa da hukumomin tsaro Amotekun da kuma rundunar soji don tsananta bincike da kuma ceto matar

- Har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto ba aji ta bakin rundunar yan sandan jihar kan lamarin ba

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sunyi garkuwa da matar Mr Olugbenga Ale, shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

An yi garkuwa da matar a yankin Owena da ke jihar Ondo a daren Alhamis, wata majiya ta tabbatarwa da SaharaReporters.

Wannan na zuwa ne awa ashirin da hudu bayan masu garkuwa da mutane sun hallaka Oba Adegoke Isreal Adeusi, wani mai sarautar gargajiya a Ifon da ke karamar hukumar Ose a jihar.

An yi garkuwa da matar shugaban ma'aikatan fadar gwamnan Ondo
An yi garkuwa da matar shugaban ma'aikatan fadar gwamnan Ondo. Hoto daga @SaharaReporters
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kotu ta yanke wa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa hukuncin shekaru 3 a gidan maza

Daya daga cikin majiyar ta shaidawa SaharaReporters cewa Mrs Ale ta na hanyar tafiyar ne lokacin da yan bindigar suka sace ta.

Ya kuma bayyana cewa yan bindigar sun ruga daji bayan garkuwa da matar.

"An yi garkuwa da matar a Owene kan titin Ondo.

"An mika rahoton ga jami'an tsaro musamman Amotekun da Sojoji don su binciki ko ina kuma ana sa ran samun nasara ba da jimawa ba."

KU KARANTA: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

Wani hadimin gwamna Akeredolu, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce lamarin ya faru da daren Alhamis.

Ya ce, "gwamna ya san abin da ya faru har ya kai ziyara gidan shugaban ma'aikata a Alagbaka da kyakkyawan shirin yadda za a saki matar cikin koshin lafiya.

"Bai ma iya gabatar da kasafin kudin 2021 a gaban majalisar jihar ba saboda faruwar al'amarin kuma ya tura daya daga cikin kwamishinoninsa don gabatar da jawabin kasafin."

Har zuwa kammala wannan rahoto ba aji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ondo Tee-Lee Ikoro ba.

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel