Majalisa ta amince da bukatar Buhari ta sakin N148bn a matsayin biyan bashi ga wasu jihohi hudu
- Majalisar dattijai ta amince da bukatar shugaba Buhari na neman a sakarwa wasu jihohi hudu kudi ₦148,141,969,161.24
- Kuɗaɗen biyan bashin kwangiloli ne da jihohin suka aiwatar amadadin gwamnatin tarayya
- Jihohin da Sanatoci suka amince a biya bashin sune kamar haka; Bayelsa, Cross River, Ondo, Osun, da Ribas
Sanatoci a ranar Talata sun sahalewa buƙatar Shugaban ƙasa, Muhammad Buhari, ta neman a biya kuɗaɗe har Naira biliyan ₦148,141,969,161.24 ga jihohin Ondo, Osun, Rivers, Bayelsa, da Cross River.
Waɗannan kuɗaɗe biyan bashin kwangilolin da suka aiwatar ne a jihohinsu amadadin gwamnatin tarayya.
Sahalewar ta biyo bayan duba da ƙorafin da kwamitin basussukan cikin gida da waje na majalisar dattijai wadda Sanata Clifford Ordia ke jagoranta.
KARANTA: Ko kadan Buhari bai damu da arewa ba yanzu; ACF da NEF sun aika sako
Ordia, a jawabin da ya gabatar, ya ce yawancin manyan titunan tarayya a jihohin da zasu ci moriyar kuɗaɗen, jihohin ne suka zuba kuɗaɗensu a aikinsu kafin gwamnatin tarayya ta kawo ɗoƙi.
Ya ce "ma'aikatar ayyuka ta kai ziyara akai akai zuwa titunan tarayya da jihohin suka kammala don dubawa ko sahihacin aikin ya kai nagartar da ake buƙata."
Sai dai Sanatan yace jihohi irinsu Cross River, Rivers, Bayelsa, da Ondo sun fara ayyukan tun shekarar 2005 zuwa yau.
KARANTA: Sunayensu: Dangote ya shigar da karar wasu ma'aikatansa guda takwas
Ya ƙara da cewa tunda jihohin sun kammala duka ayyukan, kuma sun biya dukkan ƴan kwangila, sanan ma'aikatar samarwa jama'a walwala a ɓangarenta ta tabbatar an bi duk ƙa'idojin da ya dace.
A ranar Litinin ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa Buhari ya ce gwamnatinsa za ta cire masu karɓar mafi ƙarancin albashi daga biyan harajin kuɗaɗen da suke shigo musu a wani mataki na ragewa talakawan Najeriya raɗaɗin hauhauwar farashin kayayyaki.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng