Zaben Ondo: Akeredolu ya lallasa Jegede a sakamakon kananan hukumomi 12

Zaben Ondo: Akeredolu ya lallasa Jegede a sakamakon kananan hukumomi 12

- Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo yana cigaba da samun nasara a sakamakon da ke bayyana

- A halin yanzu sakamakon kananan hukumomi 12 sun bayyana daga cikin 18 na jihar

- Akeredolu na jam'iyyar APC ke gaba inda ya bai wa babban abokin adawarsa, Jegede, tazara mai yawa

Burin Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo na tazarcewa yana cigaba da karfi a yayin da aka sanar da sakamakon zabe a kananan hukumomi 12 daga cikin 18 na jihar.

Dan takarar na jam'iyyar APC ya yi nasarar lashe zaben a kananan hukumomi 9 daga cikin 12 yayin da babban abokin hamayyarsa ya samu nasara a kananan hukumomi 3 kacal.

A halin yanzu, Akeredole yana da kuri'u 178,854 inda babban abokin hamayyarsa yake da kuri'u 141,083.

Agboola Ajayi na jam'iyyar ZPL kuwa yana da kuri'u 32,060 kuma har yanzu bai yi nasarar lashe zabe a ko karamar hukuma daya ba.

Ga sakamako daga dukkan kananan hukumomi 12 da aka samu:

KU KARANTA: Bidiyon ragargazar da dakarun soji suka yi wa 'yan bindiga a Katsina

Zaben Ondo: Akeredolu ya lallasa Jegede a sakamakon kananan hukumomi 12
Zaben Ondo: Akeredolu ya lallasa Jegede a sakamakon kananan hukumomi 12. Hoto daga @Vanguard
Asali: Facebook

Karamar hukumar Ifedore

PDP 11,852; APC had 9,350 ZLP got 1,863

Karamar hukumar Akure ta Kudu

APC- 17,277 PDP- 47,627 ZLP – 2,236

Karamar hukumar Akoko ta Kudu maso gabas

APC -9,419 PDP- 4003 ZLP -2004

Karamar hukumar Ile-Oluji Okeogbo

APC – 13,278 PDP- 9,231 ZLP,- 1,971

Karamar hukumar Akoko Kudu maso yamma

APC – 21,232 PDP -15,055 ZLP – 2,775

Karamar hukumar Irele

APC 12,643 PDP 5,493 ZLP 5,904

Karamar hukumar Akoko ta arewa maso yamma

APC -15,809 PDP -10,320 ZLP -3,477

Karamar hukumar Ondo ta Yamma

APC -6,485 PDP -4,049 ZLP-3,221

Karamar hukumar Akoko ta arewa maso yamma

APC – 16,572 PDP -8,380 ZLP-3,532

Karamar hukumar Owo

APC -35,957 PDP -5,311 ZLP- 408

Karamar hukumar Akure ta arewa

APC- 9,546 PDP- 12,263 ZLP- 1,046

Karamar hukumar Idanre

APC- 11,286 PDP- 7,499 ZLP -3,623

KU KARANTA: Bidiyon yadda aka soka wa wani wuka a rumfar zabe a Ondo

A wani labari na daban, manema labarai, wakilan jam'iyyu da kuma masu lura da zabe sun tarwatse inda suka dinga neman maboya sakamakon ruwan wutar da ake musaya tsakanin 'yan sanda da 'yan daba.

Lamarin ya faru ne a makarantar firamare ta St Peter da ke Akure a ranar Asabar. Ana amfani da makarantar firamaren wurin tattara sakamakon zaben karamar hukumar Akure ta Kudu da ke jihar Ondo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel