Jerin jihohi 5 da suka rufe makarantu sakamakon zanga-zangar EndSARS

Jerin jihohi 5 da suka rufe makarantu sakamakon zanga-zangar EndSARS

- Rikice-rikice ya barke a wasu sassan kasar yayinda ake zanga-zangar EndSARS

- Matasa dai na zanga-zanga ne domin ganin a kawo karshe cin zalin da yan sanda ke yi a kasar

- A yanzu dai jihohin Lagas, Ekiti, Ondo, Osu da Oyo sun rufe makarantu

Zanga-zangar neman kawo karshen rundunar SARS da aka fara cikin lumana na ci gaba da zama tashin hankali a wasu sassa na kasar.

Kimanin kwanaki 12 kenan da matasa suka fito domin nuna fushinsu tare da fafutuka a kan cin kashin da ake zargin rundunar yan sandan kasar da aikata wa al’umman kasar.

Lamarin ya munana ne a yau Talata, 20 ga watan Oktoba, bayan wasu yan iska sun karbe ragamar zanga-zangar da ake yi cikin lumana, sannan suka dungi barna tare da kai wa jama’a hari.

KU KARANTA KUMA: Anzo wajen: Zanga-zangar #EndSARS ta sauya zani, ta koma ta'addanci a Filato

Jerin jihohi 5 da suka rufe makarantu sakamakon zanga-zangar EndSARS
Jerin jihohi 5 da suka rufe makarantu sakamakon zanga-zangar EndSARS Hoto: MojiDelano.com
Asali: UGC

Har ila yau 'yan daba ne sun kona ofishin 'yan sanda da ke Apapa Iganmu a jihar Legas kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Har wayau, fusatattun matasa a garin Ibadan da ke jihar Oyo, sun banka wa ofishin 'yan sanda da ke Ojoo wuta kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Wannan tashe-tashe hankula ya sanya gwamnatocin wasu jiha daukar matakin rufe makarantu domin kare dalibai daga fadawa hatsari.

KU KARANTA KUMA: EndSARS: IGP ya bada umurnin baza 'yan sandan kwantar da tarzoma a jihohin Najeriya

Mu zakulo maku jerin jihohin da suka yi izinin rufe makarantu saboda zanga-zangar kamar haka:

1. Jihar Lagas

Gwamnatin jihar Legas ta umarci duk daliban jihar, na makarantar gwamnati da ta kudi, da su zauna a gida saboda tarzomar da masu zanga-zangar rushe SARS suka tayar.

Kwamishinan ilimi ta jihar, Folasade Adefisayo, wacce ta bayar da wannan umarnin, tace don tabbatar da lafiyar dalibai, malamai da kuma iyayen yara, wajibi ne su dakatar da zuwa makarantu a wannan lokacin na tsanani.

2. Jihar Ekiti

Gwamna Kayode Fayemi ya yi umurnin rufe dukkanin makarantun kudi da na gwamati a Ekiti sakamakon zanga-zanga da tashin hankali a jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar, Misis Kofoworola Aderiye ta sanar da hakan a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba.

3. Jihar Ondo

Gwamna Rotimi Akeredolu ya yi umurnin rufe dukkanin makarantu a jihar Ondo, sakamakon fusatar da masu zanga-zangar EndSARS suka yi.

Gwamnan na jihar Ondo ne ya fitar da sanarwar a shafinsa na Twitter @RotimiAkeredolu, a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba.

4. Jihar Osun

A jihar Osun iyaye sun hana yayansu zuwa makaranta bayan barkewar rikici a wajen zanga-zangar ta EndSARS.

5. Jihar Oyo

Makarantun kudi da na gwamnati a jihar Oyo sun dakatar da harkokin karatu a ranar Talata, 20 ga wata Oktoba.

Koda dai babu wata sanarwa na mahukunta kan haka, yawancin makarantun kudi sun ce hakan ya zama dole saboda mawuyacin halin da dalibai suka tsinci kansu a ciki sakamakon zanga-zangar EndSARS a manyan biranen a yau Litinin, 19 ga watan Oktoba.

A gefe guda, zanga-zangar #EndSARS da ake gudanarwa a garin Jos, babbar birnin jihar Filato, ya kaure ya zama rikici.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel