Da duminsa: Akeredolu ya lallasa Jegede, Ajayi da sauransu da tazarar kuri'u 53,380 a kananan hukumomi 14
- Dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu na jagoranci a zaben gwamnan Ondo
- Akeredolu ya bai wa abokan hamayyarsa tazarar kuri’u 52,380 a kananan hukumomi 14
- Saura kananan hukumomi hudu a fadi wanda ya lashe zaben na ranara Asabar
Har yanzu dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ne kan gaba a zaben na ranar Asabar.
Akeredolu na jagoranci da kuri’u 52,380 a kananan hukumomi 14 da hukumar INEC ta saki zuwa yanzu, jaridar The Guardian ta ruwaito.
Gwamnan mai ci ya samu kuri’u 213,251 a kananan hukumomi 14 yayinda Eyitayo Jegede ya samu kuri’u 156,871.
KU KARANTA KUMA: Zaben Ondo: PDP ta lallasa APC da tazarar ƙuri'u mai yawa a ƙaramar hukumar Akure
Mataimakin gwamnan kuma dan takarar jam’iyyar Zenith Labour Party, Hon Agboola Ajayi ya samu kuri’u 44,175.
Kananan hukumomi da suka rage hukumar zabe bata sanar ba sune Ondo West, Odigbo, Ileja da Ese Odo.
Ga sakamakon kananan hukumomi 14 da hukumar zabe ta sanar;
1. Akoko SE - APC: 9,419; PDP: 4,003; ZLP: 2,004
2. Akoko SW- APC: 21,232; PDP: 15,055; ZLP: 2,775
3. Ifedore - APC: 9,350; PDP: 11,852; ZLP: 2,775
4. Owo - APC: 35,957; PDP: 5,311; ZLP: 408
5. Ose - APC: 15,122; PDP: 8,421; ZLP: 1,083
6. Irele - APC: 12,643; PDP: 5,493; ZLP: 5,904
7. Akoko NE - APC: 16,572; PDP: 8,380; ZLP: 3,532
8. Ile Oluji - APC: 13,287; PDP: 9,231; ZLP: 1,971
9. Okitipupa - APC: 19,266; PDP: 10,367; ZLP: 10,120
10. Idanre - APC: 11,286; PDP: 7,499; ZLP: 3,623
11. Ondo East - APC: 6,485; PDP: 4,049; ZLP: 3,221
12. Akoko NW - APC: 15,809; PDP: 10,320; ZLP: 3,477
13. Akure North - APC: 9,546; PDP: 12,263; ZLP: 1,046
14. Akure South - APC: 17,277; PDP: 47,627; ZLP: 2,236
KU KARANTA KUMA: Zaben Ondo: Jerin ƙananan hukumomin da ba'a faɗi sakamakon su ba
Jimlar kuri'u:
APC: 213,251
PDP: 159,871
ZLP: 44,175
Tazarar da ke tsaninsu da wanda ke jagorancci: kuri'u 53,380.
A baya, mun ji cewa yayin da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta kammala shirin gudanar da zaben kujerar gwamna a jihar Ondo, gamayyar kungiyoyi fiye da 200 a karkashin tutar TMG (Transition Monitorin Group) sun fitar da jawabi mai karfi da yammacin Juma'a.
TMG ta bukaci INEC ta samar da na'urar Z-pad mai amfani da fasahar zamani domin samun damar aika sakamakon zabe kai tsaye daga akwatuna 3,009 da ke mazabu 203 a kananan hukumomi 18 da ke jihar Ondo.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng