Nigeria: Mabarnata sun haka fafakeken rami a titin da jirgin sama ke falfala gudu kafin ya tashi

Nigeria: Mabarnata sun haka fafakeken rami a titin da jirgin sama ke falfala gudu kafin ya tashi

- Babu tashi, babu sauka, a filin jiragen sama na Akure, babban birnin jihar Ondo, sakamakon gano wani katon rami

- Ana zargin wasu mabarnata sun bi dare sun haka katon rami a titin da jirgin sama ke yin 'gare' kafin ya tashi sama

- Ana cigaba da samun sabbin rahotannin aikata barna kala-kala da wasu batagarin matasa ke yi a sassan Najeriya

An dakatar da tashi da saukar jirage a filin jiragen sama na Akure, jihar Ondo, bayan gano wani katon rami da aka haka a titin da jirgi ke yin 'gare' kafin ya shilla sararin samaniya.

Jaridar Punch ta rawaito cewa an gano katon ramin ne a ranar Litinin kuma ana zargi wasu mabarnatan mutane ne suka haka shi.

Lamarin ya tilasta mahukunta rufe titin tare da hana jirage sauka ko tashi daga filin jirgin saman.

Hakan ya hana jama'ar da ke sufuri ta jiragen sama su shiga, ko su fita, daga garin Akure.

KARANTA: Duk da gida bai koshi ba: Nigeria za ta kai wa kasar Chadi wutar lantarki

Majiyar Punch da ke filin jirgin ta bayyana cewa ma'aikata sun gano katon ramin a daren ranar Lahadi kuma ba tare da bata lokaci ba aka rufe titin.

Kakakin hukumar kula da filayen jiragen sama na Nigeria (FAAN), Henrietta Yakubu, ta bayyana cewa an gano 'tsagewa masu zurfi' a titin da jirgi ke yin 'gare' kafin ya tashi sama a ranar Litinin.

Nigeria: Mabarnata sun haka fafakeken rami a titin da jirgin sama ke falfala gudu kafin ya tashi
Jirgin shugaban kasa
Asali: UGC

Kazalika, ta bayyana cewa an fara aikin cike ramukan da gyara bangaren titin da matsalar ta shafa.

KARANTA: Sanwo-Olu ya bayyana wadanda suka yi harbe-harben Lekki

Har yanzu ba a daina samun sabbin rahotannin tafka barna da wasu batagarin matasa ke aikatawa a sassan Nigeria ba.

Mabarnatan matasa sun cigaba da aikata kala-kalar barna a salo daban-daban duk da jami'an 'yan sanda na farautarsu tare da kama wasu daga cikinsu.

Wasu kasashe da kungiyoyi sun shawarci gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti domin binciken abinda ya haddasa irin wannan abin haushi da ke cigaba da faruwa a sassa daban-daban na Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng