Gwamna Rotimi Akeredolu ya tika Eyitayo Jegede da Agboola Ajayi da kasa

Gwamna Rotimi Akeredolu ya tika Eyitayo Jegede da Agboola Ajayi da kasa

- Gwamna Rotimi Akeredolu ya kuma doke Eyitayo Jegede a zaben 2020

- A shekarar 2016, Eyitayo Jegede ya sha kashi a hannun Gwamnan mai-ci

- Bayan haka, Rotimi Akeredolu ya lallasa ‘dan takarar jam’iyyar ZLP, Ajayi

Mai girma Rotimi Akeredolu ya lashe zaben jihar Ondo da aka yi a a ranar Asabar. Hakan na nufin gwamnan zai zarce a kan kujerar mulki har 2024.

Rotimi Akeredolu ya doke PDP, da tsohon mataimakinsa, Mista Agboola Ajayi, wanda ya yi takara a karkashin jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP).

Farfesa Abel Idowu Olayinka na jami’ar Ibadan, ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC da ‘dan takararta ne su ka samu nasara da kuri’u 292,830.

Akeredolu ya yi galaba a kananan hukumomi 15 cikin 18 da ke jihar Ondo, ya bar Eyitayo Jegede da garuruwan Akure da kuma karamar hukumar Ifedore.

KU KARANTA: Gwamnan APC ya zagaye gari bayan ya samu tazarce

Jam’iyyar PDP ta samu kuri’a 195,791 ne a zaben, yayin da ZLP ta tashi da 69,127. Ratar da ke tsakanin APC da PDP ta kai kusan kuri’u 100, 000.

Inda APC ta lashe su ne: Kananan hukumomi hudu da ke cikin yankin Akoko, Ese-Odo, Idanre, Ilaje, Oluji/Oke Igbo, Irele, Odigbo, da Okitipupa.

Haka kuma jam’iyyar APC ta doke PDP a garuruwan Ondo, Ose da karamar hukumar Owo.

‘Dan takarar APC ya doke ‘yan adawa a inda ya fi karfi, sannan kuma ya shiga har yankunan da hamayya ta ke da jama’a, ya samu kuri’u masu tsoka.

KU KARANTA: Yadda aka yi zaben Gwaman Ondo

Gwamna Rotimi Akeredolu ya tika Eyitayo Jegede da Agboola Ajayi da kasa
Rotimi Akeredolu wajen kamfe Hoto: Dail Trust
Asali: UGC

Gwamna Akeredolu ya tabuka abin kirki a garuruwan Ondo, inda ya samu kuri’a kusan 27, 000 duk da cewa daga nan ne ‘dan takarar PDP ya fito.

Shi kuwa Jegede ya tashi da kuri’a 5000 ne rak a garin gwamna mai-ci watau Awo. Bayan haka APC ta doke jam’iyyar ZLP a mahaifar ‘dan takararta.

Ba a nan kadai nasarar APC ta tsaya ba, Akeredolu ya doke Agboola Ajayi a yankin da shugaban ZLP, tsohon gwamna Olusegun Mimiko ya ke da jama’a.

Kun ji cewa ‘dan takarar na jam’iyyar APC, Rotimi Akeredolu, ya zo na farko a zaben Ondo. ‘Dan takarar PDP, Eyitayo Jegede ya sha kashi, ya zo na biyu.

Rahotanni sun tabbatar da jam’iyyun siyasa 17 ne su ka shiga wannan zabe tare da ‘yan takararsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng