Zaben Ondo: Jerin ƙananan hukumomin da ba'a faɗi sakamakon su ba
- Yayinda aka kammala zaben gwamnan Ondo, an fadi sakamakon kananan hukumomi 12 zuwa yanzu
- A yanzu haka dan takarar APC ya kawo kananan hukumomi tara, dan takarar PDP na da kananan hukumomi uku
- Saura kananan hukumomi shida a fadi wanda ya lashe zaben
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fara tattara sakamakon kananan hukumomi na karshe a zaben gwamnan Ondo da aka kammala.
Zaben ya gudana ne a runfunar zabe 3,009 a unguwanni 203 na kananan hukumomi 18 da ke jihar ta kudu maso yamma.
Zuwa yanzu, hukumar zaben ta sanar da sakamako daga kananan hukumomi 12.
Dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Rotimi Akeredolu, ya lashe tara daga cikin kananan hukumomin yayinda dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Eyitayo Jegede ya kawo sauran kananan hukumomi ukun da ya rage.
KU KARANTA KUMA: KAI TSAYE: Sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo tsakanin APC, PDP da ZLP
Babban dan takara na uku a zaben, Agboola Ajayi, na jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) bai lashe kowace karamar hukuma ba tukuna.
Jami’an INEC sun dan tafi hutu domin ba sauran kananan hukumomi damar tattarawa da kuma gabatar da sakamakonsu.
Za a dawo da sanar da sakamakon zaben karfe 9:00 na safiyar yau Lahadi, 11 ga watan Oktoba, kamar yadda hukumar zaben ta bayyana.
Ga jerin kananan hukumomi shida da suka rage domin samun wanda ya lashe zaben na gwamnan Ondo idan INEC ta dawo da tattara sakamako:
1. Karamar hukumar Ilaje
2. Karamar hukumar Ose
3. Karamar hukumar Okitipupa
4. Karamar hukumar Ese Odo
5. Karamar hukumar Ondo West
6. Karamar hukumar Odigbo
KU KARANTA KUMA: KAI TSAYE: Sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo sun fara shigowa
A gefe guda, mun ji cewa burin Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo na tazarcewa yana cigaba da karfi a yayin da aka sanar da sakamakon zabe a kananan hukumomi 12 daga cikin 18 na jihar.
Dan takarar na jam'iyyar APC ya yi nasarar lashe zaben a kananan hukumomi 9 daga cikin 12 yayin da babban abokin hamayyarsa ya samu nasara a kananan hukumomi 3 kacal.
A halin yanzu, Akeredole yana da kuri'u 178,854 inda babban abokin hamayyarsa yake da kuri'u 141,083.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng