Jerin gidajen yari 5 da aka kai wa hari a yayin zanga-zangar EndSARS
- Har yanzu matasa na zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS a sassa daban daban na kasar
- Hakan ya ba wasu bata gari damar amfani da hakan wajen kai hare-hare
- Zuwa yanzu an kai hare hare a gidajen yari biyar a jihohi hudu
Yan bata gari na ci gaba da kai hare-hare a wasu sassa na kasar yayinda ake ci gaba da zanga-zangar EndSARS a fadin kasar.
Zuwa yanzu dai an kai farmaki wasu gidajen gyara halayya da ke wasu jihohin kasar.
Legit.ng ta zakulo maku jerin gidajen yarin da aka kai wa hari tare da bayani kan hare-haren.
KU KARANTA KUMA: Yanzu: Buhari ya bada umurnin daina zanga-zanga a fadin tarayya
Gidan yarin Warri da ke jihar Delta
Mun samu labarin cewa fursunoni sun saka wuta a wani bangare na gidan yarin Warri da ke kan titin Okere a jihar Delta.
Kakakin hukumar kula da gidajen yari ta kasa (NCS), DSP Onome Onovwakpoyeya, ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kara da cewa mahukuntan gidan yarin ba su da masaniyar ko wani Fursuna ya tsere.
The Nation ta ruwaito cewa wasu Fursunoni da ba a san adadinsu ba sun tsere daga gidan yarin na Okere duk da harbe-harben da jami'an tsaro ke yi.
KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin albashin 'yan sanda na zuwa nan babu dadewa - Buhari
Gidan yarin Okitipupa da ke jihar Ondo
A ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba ne wasu bata gari suka kai farmaki gidan yari da ke Okitipupa, hedkwatar karamar hukumar Okiyipupa da ke jihar Ondo.
A cewar rahoton Channels TV, akalla fursunoni 58 sun gudu daga gidan gyara halin kuma sun bankawa gidan yarin wuta dake karamar hukumar Ikitipupa na jihar.
Gidan yarin Ikoyi da ke jihar Lagas
A yau Alhamis ne jami'an yan sanda da Sojoji suka dira gidan gyaran halin a unguwar Ikoyi da ke jihar Legas domin dakile yunkurin fitar da fursunoni da wasu bata gari ke yi yanzu haka.
An gano wasu bangarori na kurkukun na ta ci da wuta yayinda mutanen yankin ke neman mafaka don tsiratar da rayuwarsu, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
Sai dai bata garin basu cimma manufarsu ba domin jami’an tsaro sun yi nasarar dakile harin.
Gidajen yari na Benin da Oko a jihar Edo
A ranar Litinin ne hukumar gyaran gidan hali ta Najeriya ta tabbatar da harin gidajen yari a hanyar Sapele da ke Benin da Oko duk a jihar Edo, jaridar Premium Times ta ruwaito.
Fursunoni 1,993 ne suka gudu bayan harin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng