Zaben Ondo: PDP ta lallasa APC da tazarar ƙuri'u mai yawa a ƙaramar hukumar Akure
- Dan takarar gwamna na PDP, Jegede, ya lallasa abokan hamayyarsa a kananan hukumomin Akure ta kudu da Akure ta arewa
- A Akure ta Kudu, dan takarar na PDP ya samu kuri’u 47,627 wajen lallasa Akeredolu wanda ya samu kuri’u 17, 277
- Hakazalika, Jegede ya samu kuri’u 12,263 waje kayar da dan takarar APC wanda ya samu kuri’u 9,546
Eyitayo Jegede, dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Ondo ya samu gagarumin nasara a kananan hukumomi biyu na Akure ta Kudu da Akure ta Arewa.
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ce ta sanar da sakamakon a safiyar ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba.
A Akure ta Kudu, Jegede ya samu kuri’u 47,627 wajen kayar da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Rotimi Akeredolu, wanda ya samu kuri’u 17, 277.
Dan takarar jam’iyyar Zenith Labor Party (ZLP), Agboola Ajayi, ya samu kuri’u 3,623 a wannan karamar hukumar.
KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Ɗan sanda ya shiga sahun zanga zangar ruguza rundunar FSARS
A Akure ta Arewa, Jegede ya samu kuri’u 12,263 wajen kayar da Akeredolu wanda ya samu kuri’u 9,546 da Ajayi wanda ya samu kuri’u 1,046.
Rabe-raben kuri’unya nuna cewa Jegede ya lallasa abokin hamayyarsa na kut-da-kut da kuri’u 3,067 a Akure: 30.350 a kudu sannan 2,717 a arewa.
KU KARANTA KUMA: Zaben Ondo: Akeredolu ya lallasa Jegede a sakamakon kananan hukumomi 12
Ana ganin kananan hukumomin biyu sune inda dan takarar na PDP ya fi karfi.
Jegede ya fito daga yanki Ondo ta tsakiya wanda ya hada da kananan hukumomin Akure ta kudu, Akure a Arewa, Ifedore, Idanre, Ondo yamma, da kuma Ondo ta gabas.
A gefe guda, mun kawo maku cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fara tattara sakamakon kananan hukumomi na karshe a zaben gwamnan Ondo da aka kammala.
Zaben ya gudana ne a runfunar zabe 3,009 a unguwanni 203 na kananan hukumomi 18 da ke jihar ta kudu maso yamma.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng