Da ɗuminsa: APC ta kori ƴar majalisar ta mace tilo saboda zargin cin amana

Da ɗuminsa: APC ta kori ƴar majalisar ta mace tilo saboda zargin cin amana

- Jam'iyyar APC babin jihar Ondo ta fatattaki wata mambanta mai wakiltan mazabar Ilaje, Hon. Tomomewo Favour

- APC ta dakatar da Favour, wacce ta kasance mace daya da take da ita a majalisar dokokin Ondo bisa zargin yi wa jam'iyyar zagon kasa

- Shugaban jam'iyyar na unguwarsu ‘Mahin ward IV’ ne ya sallame ta

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen Ondo ta dakatar da yar majalisa mace daya tilo da ta ke da ita a majalisar dokokin jihar, Hon. Tomomewo Favour.

Shugaban jam’iyyar na unguwar ‘Mahin ward IV’ ne ya dakatar da yar majalisar mai wakiltan mazabar Ilaje.

Dakatarwar nata ya biyo bayan zarginta da ake da cin amanar jam’iyyar kafin da lokacin zaben gwamnan jihar Ondo da aka kammala.

KU KARATA KUMA: Ta’addanci: Yan gudun hijira na iya komawa Baga domin akwai tsaro yanzu, gwamnatin Borno

Da ɗuminsa: APC ta kori ƴar majalisar ta mace tilo saboda zargin cin amana
Da ɗuminsa: APC ta kori ƴar majalisar ta mace tilo saboda zargin cin amana Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

Wasikar korar nata mai kwanan wata 12 ga watan Oktoba, na dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na unguwa, Olamigoke Ajimuda da kuma na sakataren unguwa, Omosule Taid.

Yar majalisar ta kasance daya daga cikin mambobin majalisar dokokin da suka nuna adawa da kokarin tsige mataimakin gwamna, Hon Agboola Ajayi, watanni biyu da suka gabata, jaridar Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Akalla mutane 10 sun mutu a zanga-zangar #ENDSARS kawo yanzu

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya bukaci ayi ta ta kare tsakaninsa da gwamna Samuel Ortom ba tare da an kai ga kotu ba.

Kwanaki gwamnan jihar Benuwai Samuel Ortom ya maka Adams Oshiomole a kotu, ya bukaci ya biya sa Naira biliyan 10 bisa zargin yi masa karya.

Idan za ku tuna a watan Yulin 2018 ne Adams Oshiomole ya kira taron manema labarai, inda ya zargi Samuel Ortom da hannu a kisan wasu fastoci biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng