Hotunan Akeredolu da mataimakinsa suna murnar nasarar da suka samu
- Akeredolu Rotimi da mataimakinsa Lukcy, sun zagaye titunan Owo domin shagalin murnar nasararsu
- A ranar Asabar, 10 ga watan Oktoban 2020 jama'ar Ondo suka fita kada kuri'unsu domin zaben gwamna a jihar
- Bayan fafatawa, a ranar Lahadi hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana Gwamna Akeredolu a matsayin wanda yayi nasara
Gwamnan jihar Ondo, Gwamna Rotimi Akeredolu tare da Lucky Aiyedatiwa, mataimakinsa, sun zagaya titunan Owo domin shagalin bikin murnar nasara da suka samu a zaben gwamnoni da aka yi a ranar Asabar.
Idan za mu tuna, jama'ar jihar Ondo sun fita kwansu da kwarkwata a ranar 10 ga watan Oktoban 2020 domin kada kuri'ar samun wanda zai jagorancesu na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Jam'iyyun siyasa 17 ne suka fitar da 'yan takara amma jam'iyyu uku ne suka fi daukar hankali.
Akwai jam'iyyar APC wacce Akeredolu ne dan takara kuma gwamna mai gadon mulki, sai Jegede Ajayi na jam'iyyar PDP wanda shi ne babban abokin hamayya, sai kuma dan takarar ZLP, Agboola.
Gwamna ya dinga nuna farin cikinsa tare da annashuwar gagarumar nasarar da ya samu ta lallasa babban abokin hamayyarsa da kusan kuri'u dubu dari.
KU KARANTA: Ku yi rayuwa mai kyau, ko za ku samu makoma kyau - Obasanjo ya shawarci 'yan Najeriya
KU KARANTA: EndSARS: Dawisu, hadimin Ganduje, ya yi wa Buhari wankin babban bargo
A wani labari na daban, Rotimi Akeredolu ya yi nassarar lashe zaben gwamnoni na jihar Ondo. Akeredolu na jam'iyyar APC ya samu nasarar samun kuri'u 292,839 yayin da Eyitayo Jegede na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 193,585.
An samu tazarar kuri'u 99,254 a tsakanin jam'iyyar APC da PDP. Agboola Ajayi na jam'iyyar ZLP ya bayyana a na uku inda ya samu kuri'u 60,051.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng