Cire Tallafin Man Fetur Na Tinubu: NLC Ta Fara Zanga-Zanga Na Gama-Gari (Kai Tsaye)

Cire Tallafin Man Fetur Na Tinubu: NLC Ta Fara Zanga-Zanga Na Gama-Gari (Kai Tsaye)

Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC, ta fara zanga-zanga a sassa daban na Najeriya bisa matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka na cire tallafin man fetur a kasa ba tare da 'gamsassun' hanyoyin rade wa al'ummar kasar radadi ba.

Tun bayan da Shugaba Tinubu ya ayyana cewa 'tallafin mai ya tafi' a yayin jawabinsa na ranar rantsuwar kama aiki, farashin kayayyaki da ayyuka a kasar suka fara tashin gwauron zabi musamman abinci da sufuri.

Hakan ya biyo bayan karin kudin man fetur da yan kasuwa da NNPCL suka yi bayan cire tallafin.

Zanga-zangar ku zai iya tsayar da tattalin arzikin kasa, Majalisa ta fada wa NLC

Majalisar Dattawa ta bukaci masu zanga-zangan sun dakatar da zanga-zangansu kuma su bada damar a cigaba da tattaunawa.

Ali Ndume, sanata daga Borno, wanda ya yi magana a madadin majalisar, ya fada wa ma'aikatan cewa zanga-zangansu zai kara janyo tabarbarewar abubuwa ne a kasar, The Nation ta rahoto.

Sanatoci sun yi wa masu zanga-zangan NLC jawabi

Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya jagoranci wasu takwarorinsa yayin da suka yi magana da ma'aikatan.

Hakan na zuwa ne bayan ma'aikatan sun balle kofar majalisar sun shiga harabar.

Bidiyon ma'aikata suna wakokin hadin-kai bayan balle kofar majalisa

Mambobin kungiyoyin kwadago wadanda suka balle kofar majalisa sun rika rera wakokin hadin kai bayan shiga harabar majalisar.

A bidiyon da ya bazu an gansu dauke da takardu masu rubutu a harabar majalisar.

Za mu 'kori' Tinubu da zanga-zangar mu

Kungiyoyin kwadagon sun sha alwashin fatattakar Shugaba Tinubu daga ofis idan ya gaza biya musu bukatunsu.

Igboji Chidi, shugaban TUC na jihar Ebonyi ya furta hakan a Abakaliki, babban birnin jihar.

Masu zanga-zanga sun balle kofar majalisar tarayya, sun shiga

Mambobin NLC da ke zanga-zanga sun balle kofar majalisar tarayya sun shiga harabar.

Channels Television ta rahoto a ranar Laraba cewa lamarin ya faru yayin da ake zanga-zangar adawa da cire tallafin man fetur.

Muna son a fara biyan N200k a matsayin albashi mafi karanci, NLC ta fada wa Tinubu

NLC ta nemi shugaban kasa ya yi bitar albashi a kasar ya kara mafi karanci zuwa N200k.

Ayuba Suleiman, shugaban NLC na Kaduna, yayin zanga-zangan a ranar Laraba, ya kuma nemi gwamnati ta dawo da tallafin man fetur din da wasu suka ce yana rusa tattalin arzikin kasar.

Duba bidiyon a nan:

NLC ta Jihar Oyo ta shiga zanga-zanga

Kungiyar NLC reshen jihar Oyo ta shiga zanga-zangan da ake yi a duk fadin kasa kan neman FG ta dawo da tallafin man fetur.

Vanguard ta rahoto a ranar Laraba cewa mambobin kungiyan sun taro a gaban sakatariyar jihar tare da jami'an tsaro.

Yan NLC sun hana ababen hawa zirga-zirga a Cross River

Mambobin kungiyoyin kwadago a Cross Rivers sun taru a Calabar, babban birnin jihar kan batun neman dawo tallafin man fetur.

Ma'aiktan suna tare rera wakokin zanga-zanga don nuna bacin ransu.

Ga bidiyon a kasa:

Mambobin NLC ba su fito ba sosai a Imo

Kungiyar NLC reshen jihar Imo ta fito zanga-zanga kamar yadda takwarorinta na jihohi suka fito.

Amma, bidiyon zanga-zangan da Channels ta wallafa a ranar Laraba ya nuna cewa da dama cikin yan kungiyan ba su fito ba.

Ga bidiyon a kasa:

Shugaban NLC da TUC sun jagoranci zanga-zanga a Abuja

Joe Ajaero, shugaban NLC na kasa da takwararsa na TUC suna jagorantar zanga-zangar adawa da cire tallafin man fetur a Abuja, babban birnin Najeriya.

A cewar The Nation, kungiyoyin kwadago da kungiyoyin kare hakkin al'umma sun taro a shatale-talen fountain da ke Abuja, a ranar Laraba, 2 g watan Agusta sun karfe 7 na safe.

NLC ta rufe hanyoyi, ta yi tattaki na yanci, bidiyo ya bayyana

An hangi mambobin NLC a Legas suna wakoki na karfafa wa juna gwiwa da hadin kai.

A cewar kungiyar, shugaban kasa ya janye tallafin man fetur da ya cire, duk da cewa masu fashin baki da dama sun ce tallafin na rusa tattalin arzikin kasar.

Duba bidiyon a kasa:

Mambobin NLC sun taru a Legas, sun fara zanga-zanga

Mambobin kungiyar kwadago NLC, a ranar Laraba, 2 ga watan Agusta sun fara zanga-zanga kan cire tallafin man fetur.

Kamar yadda hotunan da The Cable ta wallafa suka nuna, masu zanga-zangan sun taru yayin da jami'an tsaro ke kusa da su don sa ido.

Online view pixel