Har An Fara Murna, Sai AA Rano Ya Musanta Karya Farashin Litar Fetur Daga N540

Har An Fara Murna, Sai AA Rano Ya Musanta Karya Farashin Litar Fetur Daga N540

  • Kamfanin A. A Rano ya musanya labarin da ake yadawa cewa ya karya farashin fetur a gidajen mai
  • A daren yau aka yi ta yada labari wai ana saida litar man fetur a gidajen man ‘dan kasuwan a kan N400
  • Ko da mafi yawanmutane ba za su so jin hakan ba, gaskiyar magana ita ce kudin lita bai canza ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A yammacin Laraba, 5 ga watan Yuli 2023, rade-radi su ka fara yawo cewa kamfanin A. A Rano ya karya farashin man fetur.

Kafin a je ko ina, kamfanin man ya yi maza-maza ya musanya wannan magana, ya nuna cewa babu alamar gaskiya tattare da batun.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa sanarwar ta fito ne daga wani shafi da mu ke kyautata zaton na kamfanin A. A Rano Nigeria Ltd ne.

Kara karanta wannan

An Rasa Inda Tattalin Arziki Ya Dosa, Za a Shafe Kusan Kwanaki 60 Babu Ministoci

Fetur
Fetur a gidan AA Rano a Kaduna Hoto: @aaranonigeria
Asali: Twitter

Gajeren jawabin da aka fitar da kimanin karfe 10:00 na daren yau ya tabbatar da farashin mai yana nan yadda aka san shi a kamfanin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba tare da wani kame-kame ba, kamfanin ya ce babu inda yake saida litar man fetur dinsa a kan N400 a duk gidajen man da yake Najeriya.

Labarin bogi mai karkatarwa

"Shugabannin kamfanin AA Rano su na masu karyata wani bayani na karya kuma mai batarwa dangane da saida man fetur a kan N400 a wasu zababbun gidajen mai.
Ayi watsi da wannan labari na karya kaco-kam dinsa."

- Kamfanin AA Rano Nigeria Ltd

Kash, ina ma da gaske ne

Bisa dukkan alamu dai wannan jawabi bai yi wa mutane dadi ba. Har wasu sun fara murna da jin ana rade-radin farashin fetur ya sauka.

A labarin karyar da ake yadawa, an daura hoton Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, ana yi masa addu’o’i saboda tunanin ya sawakewa talaka.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Muna Dab Da Durkushewa, Dillalan Mai Sun Bayyana Irin Halin Kunci Da Suke Ciki, Sun Nemi Agaji

Lissafin ba zai fita ba

Attajirin ‘dan kasuwar wanda ya fara harkar mai tun a 1994 ya yi suna wajen saida fetur da araha, ana masa kallon wanda bai tsawala farashi.

Amma duk da haka zai yi wahala fetur ya koma N400 domin bincikenmu ya nuna mana litar danyen man Najeriya a yau a ketare ya kai N360.

Kafin fetur ya shigo gidajen mai sai an kashe kudin jigila, tacewa da dakonsa daga waje. Da kamar wahala a saida fetur a haka, har a ci riba.

Fetur zai iya haura N540

Rahoto ya zo cewa kungiyar OPEC ta na shirin rage adadin danyen man da ake hakowa. A halin yanzu farashin litar fetur bai wuce N540 ba.

Watakila litar fetur ya kara tsada idan Saudi Arabiya ta yi nasarar tashin kudin ganga a kasuwar Duniya, hakan zai yi tasiri a aljihun mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel