Labaran NNPC
Kamfanin NNPCL ya yiwa kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) martani kan cewa ya na adawa da matatar man Dangote. NNPCL ya ce Dangote zai iya sayarwa 'yan kasuwa mai.
Kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya bayyana cewa man matatar Ɗangote zai soma shiga kasuwa ranar 15 ga watan Satumba, kuma kasuwa ce za ta kayyade farashinsa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba matsalar karancin man fetur za ta zama tarihi a kasar nan. Ta ba 'yan Najeriya tabbaci.
Yan acaba da masu Keke Napepe sun yi zanga zangar adawa da karin kudin mai a jihar Kwara. Sun bukaci Bola Tinubu ya rage kudin mai a fadin Najeriya.
Aliko Dangote ya ce har yanzu bai yanke hukunci kan yadda farashin man fetur zai kasance a matatarsa ba. Ya ce maganar ya fara sayar da mai a N897 ba gaskiya ba ce.
Karin kudin man fetur da kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya yi, ya jawo masu sana'ar adaidaita sahu da sauransu sun yi karin kudi ga fasinjoji a Kaduna.
'Yan majalisa marasa rinjaye na majalisar wakilai sun yi Allah wadai da karin kudin man fetur da aka yi. Sun bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta cire karin.
Kungiyar MAN ta ce da yiwuwar farashin kayayyaki ya kara hauhawa sakamakon ƙaruwar kuɗin litar man fetur a Najeriya, ta ce kananan sana'o'o zasu shiga matsala.
Rahotanni sun bayyana cewa druruwan 'yan adaidaita sahu sun mamaye titunan Kano domin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da karin farashin man fetur.
Labaran NNPC
Samu kari