Daga Karshe Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Lokacin da Fetur Zai Wadata

Daga Karshe Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Lokacin da Fetur Zai Wadata

  • Gwamnatin tarayya ta ba da tabbacin cewa akwai isashshen man fetur da zai wadaci ƴan Najeriya
  • Ƙaramin ministan fetur wanda ya ba da wannan tabbacin ya ce matsalar ƙarancin mai za ta zo ƙarshe zuwa nan da ƙarshen mako
  • Sanata Heineken Lokpobiri ya bayyana cewa farashin man fetur ɗin zai bambanta a wasu wurare amma komai zai daidaita daga baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi magana kan matsalar ƙarancin man fetur da ake fama da ita a ƙasar nan.

Gwamnatin tarayyar ta bakin ƙaramin ministan man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri ta ba ƴan Najeriya tabbacin cewa nan ba da jimawa matsalar za ta zama tarihi.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya ba Tinubu shawarar abin da ya kamata ya yiwa ministocinsa

Gwamnati ta magantu kan karancin fetur
Gwamnatin tarayya ta ce matsalar karancin fetur ta kusa zuwa karshe Hoto: @OfficialABAT, @senlokpobiri
Asali: Twitter

Ƙusoshin gwamnati sun gana kan ƙarancin fetur

Sanata Lokpori ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala ganawa da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙaramin ministan na man fetur ya sanya tattaunawar ta sa da manema labaran ne a shafinsa na X.

Tattaunawar dai na zuwa ne bayan Kashim Shettima ya gana da ministan da shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) Mele Kyari da Nuhu Ribadu kan matsalar ƙarancin man da ake fuskanta.

Me gwamnati ta ce kan ƙarancin fetur?

"Abin da ke da muhimmanci shi ne akwai isashshen fetur a ƙasa, kuma mun yi amanna cewa daga yanzu zuwa ƙarshen mako, man fetur zai wadata a dukkanin faɗin ƙasar nan."
"Farashin zai bambanta a wasu wuraren, wasu wuraren za a same shi da tsada."

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun yi martani kan karin kudin fetur, sun ba gwamnati shawara

"Amma mun yi amanna cewa zuwa lokacin da fetur zai gama wadata a faɗin ƙasar nan, farashin zai daidaita."

- Sanata Heineken Lokpobiri

Zanga-zanta ta ɓarke kan tsadar fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa zanga zanga ta ɓarke a jihar Kwara domin nuna ƙin amincewa da ƙarin kuɗin man fetur da aka yi a Najeriya.

Masu sana'ar ahaɓa da adaidaita sahu ne suka yi zanga zanga tare da daina daukan mutane biyo bayan tashin gwauron zaɓi da farashin fetur.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng