Matasan Najeriya
Gwamnan jihar Jigawa ya dauki hadimai kusan 200 a yayin da ake fama da wahalar rayuwa a Najeriya. Sakataren gwamnatin jihar, Bala Ibrahim ne ya sanar.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta tarwatsa wasu matasa da suka yi kokarin fasa wuraren adana kaya da wasu shagudan a' Zoo Road' da ke birnin Kano.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin kin sanar da wuraren siyar da shinkafa mai nauyin 50kg kan kudi N40,000 kacal inda ta ce ta yi hakan ne domin dalilai na tsaro.
Gwamnonin jihohi sun ja kunnen masu zanga zanga su bi hankali ban da yin duk wani abu da zai iya kawo tashin tashin a tsawon lokacin da za su ɗauka.
Mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara ya yi wakar martani bayan goge shafinsa na Facebook da talakawa suka nema a yi a kan wakar Bola Tinubu cikin sabuwar waka.
A ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta, matasa za su hau kan tituna domin yin zanga zangar adawa da manufofin gwamnati da suka haifar da tsadar rayuwa.
Omoyele Sawore, ɗaya daga cikin masu jan ragamar shirya zanga zangar lumana da za a yi yau ya musanta raɗe-raɗin cewa an ɗage zanga zangar zuwa watan Oktoba.
Mai ba shugaban ƙaa shawara kan harkokin ɗalibai, Sunday Asefun ya ce suna zargin wasu masu ƙarfin juya gwamnati da ake ce ma Cabals da hannu a zanga zanga.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakile masu shirin gudanar da zanga-zanga a gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024 inda ta ce a filin wasa kawai za su tsaya.
Matasan Najeriya
Samu kari