Matsaloli 7 da Kwana da Garwashi a Daki Kan Iya Jawowa Mutum, Sai a Kula

Matsaloli 7 da Kwana da Garwashi a Daki Kan Iya Jawowa Mutum, Sai a Kula

  • An ce lafiya uwar jiki, amma a nemawa jiki lafiya wasu ke tsoma kawunansu cikin wata matsalar ta lafiya
  • Kunna gawarshi a kwana dashi ba sabon abu bane, mutane sun dauki hakan a matsayin mafita ga matsalar sanyi
  • Sai dai, masana kiwon lafiya sun ba da shawarin a guji kwana da garwashi a daki, hazan na da matsala ga dan Adam

Yayin da sanyi ke ci gaba da busawa a duniya, mutane da yawa na amfani da garwashi wajen dumama daki don samun damar zama cikin tsanaki.

Sai dai, shin kunsan hakan na da illa ga lafiya? Masana sun yi tsokaci game da wannan lamari, sun kuma fadi mafita.

A wata hira da BBC Hausa ta yi da Dr. Hadiza Ashiru, batutuwa sun fito na illolin da ke tattare da kwana da garwashin wuta a daki.

Kara karanta wannan

"Wa Ya Aike Shi": Bidiyon Ango Ya Fadi Kasa Yayin Kokarin Daukar Matarsa Yayin Da Suke Rawa A Ranar Aurensu

Matsalolin da ke tattare da amfani da garwashi a kwana dashi a daki
Matsaloli 7 da Kwana da Garwashi a Daki Kan Iya Jawowa Mutum, Sai a Kula | Hoto: needpix.com
Asali: UGC

Ta fadi illoli bakwai da ka iya samun mutumin da ke kwana da garwashi, karshe kuma ta ba da shawarin yadda za a samu sauki a wannan sanyin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Illoli 7 na kwana garwashi

Ga illolin da ta bayyana kamar haka:

1. Jawo Gobara

Sanya garwashi a daki a kwana dashi yana iya haifar da gobara da ka iya kaiwa ga asarar dukiya da ma rai.

2. Garwashi na dauke da guba

Kwana da garwashi na iya haifar da illa ta lafiya, domin duk da rashin warinsa, yana tartsatso da sinadarin carbon mono oxide; mai illa ga huhu.

3. Matsalar numfashi

Ga masu cututtuka irinsu Asma, kwana da garwashi zai iya tada cutar ko kuma ya kai ga kisa.

4. Toshe hanyoyin iska

Sannan, kwana da garwashi zai iya jawo shakewar hanyoyin iska da ka iya kaiwa ga mutuwa.

Kara karanta wannan

Kebbi: Jirgin Ruwa ya Nitse da Sama da Mutum 100, Manoma 10 Sun ce ga Garin ku

5. Cutar da fata

Kwana da garwashi a daki zai iya busar da fata, daga nan ya haifar da mutuwar wasu abubuwan da ke kanta.

6. Cutar mantuwa

Hayakin da garwashi ke fitarwa zai iya haifar da cutar da ke da alaka da mantuwa.

7. Matsalar kwakwalwa

Ga mutanen da suka fara tsufa, amfani da garwashi a kwana dashi a daki kan iya haifar da cutar da za ta iya taba kwakwalwa duk dai ta sanadiyyar hayakin da ke fita.

Meye mafita?

Da take bayyana abin da ya kamata mutane su yi, Dr Hadiza ta bayyana cewa, babu laifi mutum ya kunna garwashi, a bude tagogin daki domin hayakin ya fita, amma kuskure ne kwana dashi.

Duba da illolin da ke tattare da wannan garwashi, ta shawarci jama’a da su kauracewa yawan amfani dashi don kwana ana jin dumi a dakuna.

Hakazalika, ta ce mafi kyau shine amfani da rigar sanyi, hula, safa kda bargo mai kauri wajen kwanciya don yakar dukkan sanyi.

Kara karanta wannan

Dandazon Masoya Sun Dira Ribas a Fatakwal Yayin Da Portable Ya Yi Waka A Tsakiyar Rafi, Bidiyon Ya Bazu

A makon nan ne aka tsinci gawarwakin ma'aurata a Kano saboda kwana da garwashi da suka yi a daki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel