Yadda Aka Kashe Matashi Yana Ƙoƙarin Tallata Sabon Addini a Arewacin Najeriya

Yadda Aka Kashe Matashi Yana Ƙoƙarin Tallata Sabon Addini a Arewacin Najeriya

  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu fusatattun matasa a kauyen Nasaru da ke jihar Bauchi sun halaka wani matashi a ranar Laraba
  • Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ce an kashe matashin mai suna Yunusa Usman a lokacin da yake tallata sabon addini
  • Mun tattauna da wani malamin addini Musulunci, wanda ya yi magana bayani kan halaccin irin wannan kisan da aka yi wa matashin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Bauchi - Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da wani mummunan lamari da ya faru a kauyen Nasaru a ranar Laraba, wanda ya yi sanadin mutuwar wani matashi.

A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar Bauchi, Ahmed Wakili, wani matashi mai suna Yunusa Usman ne aka kashe saboda tallata sabon addini.

Kara karanta wannan

Sata kirikiri: Yadda aka kwamushe ma'aikatan banki 2 da zargin sace kudi a asusun mamaci

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan matashin da aka kashe a Bauchi
An kashe matashi mai tallata sabon Addini a jihar Bauchi. Hoto: Legit.ng
Asali: Twitter

An kashe matashi mai tallar addini

Ahmed Wakili ya bayyana cewa matashin ya fara yiwa mazauna kauyen da'awar addinin 'Fera Movement', lamarin da ya harzuka su, suka kashe shi, in ji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Auwal Muhammad, ya yi kakkausar suka ga abin da masu hannu a kisan matashin suka aikata, inda ya jaddada muhimmancin bin doka da oda.

Rundunar ‘yan sandan ta sha alwashin kara sanya ido a yankin domin tabbatar da tsaro da kuma ganin cewa wannan lamarin bai haifar da tashin tarzoma ba.

Ana zargin Yunusa da kalaman batanci

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wasu fusatattun matasa ne suka yiwa marigayi Yunusa Usman dukan tsiya har ya mutu saboda furta kalaman batanci.

An zargi Yunusa da furta kalaman batanci a kan Annabi Muhammad (S.A.W). Wani ganau daga kauyen Nasaru ya yi ikirarin cewa:

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Gingima-gingiman lauyoyi sun soki hukuncin kotu, sun zargi ƴan siyasa

"Wasu samari sun nemi Yunusa da ya janye kalamansa, amma ya ki yin hakan. Har ma ya nanata kalaman nasa. A lokacin ne suka fara dukansa.”

Ya hallata kisan da aka yi wa matashin?

Ko da muka tuntubi wani malamin addinin Muslunci, Goni Abubakar Saeed Funtua, kan halaccin kisan da aka yi wa matashin, ya ce yin hakan ba dai dai bane.

Goni Abubakar ya yi nuni da cewa ba a kashe wata rai ba tare da haddi ba, kuma ya ce dole shari'a ce za ta iya yanke hukuncin kisa ba wai mutane gama gari ba.

Malamin addinin ya ce kuskure ne mutane su hau dokin zuciya, su rika yanke ɗanyen hukunci irin wannan, wanda ka iya jawo fushin ubangiji a kan al'umma.

Ya yi kira ga daukacin al'ummar Musulmi, da su kasance masu mika ire-iren waɗannan lamuran ga hukumomin da suka dace domin daukar matakin da ya dace.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun tura sako bayan kisan wanda ya ƙirkiro addini a Bauchi

An hallaka mai batanci a Sokoto

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu mutane sun yi ajalin wani mahauci mai suna Usman Buda wanda ake zargin ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Wani jami'in tsaro da ya bukaci a boye sunansa ya bayyana cewa marigayin yana zama ne a Gidan Igwe da ke karamar hukumar Sokoto ta Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.