Matasan Najeriya
Gwamnatin Kaduna ta ce babu wata dokar hana fita da aka sanya a jihar. Uba Sani ya ce yanzu an dawo da kwanciyar hankali a jihar bayan ta'addancin masu zanga-zanga.
Matasan Najeriya masu zanga zanga a dandalin Eagle Square sun dakile ministan matasa, Ayodele Olawande daga yin magana yayin da suke zanga zanga a Abuja.
Ana cigaba da zanga-zanga a fadin Najeriya baki daya inda a halin yanzu ya rikide ya koma tashin hankali a manyan biranen Arewacin kasar a yau Alhamis.
Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana fita har na tsawon awanni 24 domin dakile barnar da ake yi yayin da ake cigaba da zanga-zanga a fadin jihar.
Gwamnatin jihar Yobe ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yankunan Potiskum, Gashua da Nguru na jihar bayan da wasu ‘yan daba suka kwace zanga-zanga.
Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa masu zanga-zanga a birnin Abuja sun durfafi yankin Asokoro inda ke dauke da manyan kasar Najeriya a yau Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga zanga sun farmaki ofishin hukumar KASTLEA da ke jihar Kaduna inda suka cinna masa wuta tare da wawushe dukiyar jama'a.
Rahotanni sun bayyana cewa zanga-zanga a Kano ta rikide zuwa fitina yayin da aka kashe wani matashi a Hoto, inda wani matashin kuma ke kwance bayan harbin bindiga.
Rundunar yan sanda a jihar Kaduna sun yi yunkurin bude kwanar Gwargaje da matasa masu zanga zanga suka toshe. Yan sanda sun fesa borkonon tsohuwa ga matasan.
Matasan Najeriya
Samu kari