Bidiyon Magidanci Kwance Share Share a Bayan Mace Tana Tuka Babur Ya Jawo Cece Kuce

Bidiyon Magidanci Kwance Share Share a Bayan Mace Tana Tuka Babur Ya Jawo Cece Kuce

  • An ga wani mutum share-share ya baje yana bacci a bayan wata mata tana tuka babur yayin da suke yawo a titi, lamarin da ya jawo magana
  • Matar tana tuka babur din ne a kan babban titi yayin da mutumin ke zaune a bayanta kuma kansa yana kan kafadarta alamar yana bacci
  • A cikin faifan bidiyon mutumin da ya yadu a intanet an ji sautin dariyar wanda ke daukar bidiyon yayin da ya ke tsokanar magidancin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jama'a sun yi martani daban daban kan bidiyon wani mutum da ya dage yana sharar bacci a kafadar wata mata.

An dai ga mutumin ya zauna cikin kwanciyar hankali yayin da matar ke tuka babur din kamar za ta kai shi gida.

Bidiyon magidanci kwance share-share a bayan mace tana tuka babur
Bidiyon magidanci kwance share-share a bayan mace tana tuka babur. Hoto daga TikTok/@prettyomah48.
Asali: TikTok

Magidanci ya yi rashe-rashe bayan mace

A wani bidiyon TikTok, an ga macen dake tuka babur din kan babban titi, kuma jama'a sun dinga ihu a duk inda matar da mutumin suka wuce.

Kara karanta wannan

Sanata ya bayyana abin da yasa Tinubu ya gagara shawo kan tsadar abinci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin kuwa ya nuna ko gezau bai san suna yi ba amma yayin da mutane suka dinga ihu, ya bude idanuwansa tare da shekewa da dariya.

Ma'abota shafukan sada zumunta sun yi martani kan wannan bidiyo da ya yadu inda wasu ma ke zargin cewa mutumin ya sha ya bugu ne, sai dai ba su tabbatar ba.

Wata 'yar TikTok, @prettyomah48 ce ta saka bidiyon a shafinta, kalla a kasa:

Martanin jama'a kan bidiyon mutumin a babur

@PrettyJay ta ce:

"Daga alama ta dauko shi ne daga mashaya."

@Mompere yace:

"Ya samu kwanciyar hankali da matarsa."

@Qweenie3312 ta ce:

"Daga gidan giya taje ta dauko mijinta saboda ya bugu, lallai an ga soyayya."

@Eziagbo ya ce:

"Kwanciyar hankalin mace ta gari kamar na uwa ne. Gaskiya ku bar shi ya mori kwanciyar hankalinsa."

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya za ta canja matsugunnin wasu gidajen gyaran hali, ta fadi dalili

@jenom101_on_ig ya ce:

"Samun mace wacce za ta baka kwanciyar hankali a wannan zamanin sai ka yi sa a."

@Richie milz ta ce:

"Irin wadannan mazan ne suke kiran matansu da mama."

@Daddyoo billion ya ce:

"Irin wannan dadin kake ji idan ka auri rabin ranka."

"Dalibaina ke kirana Biri" - 'Yar Najeriya

A wani labari na daban, mun bayyana muku yadda wata 'yar Najeriya mai koyarwa a Japan ta koka da nuna mata banbancin launin fata da ake yi.

A wani bidiyo da ta fitar, ta bayyana yadda dalibanta ke kiranta da biri a Japan inda take koyarwa lamarin da ya sa ta rika sharbar kuka tana ba mutane labari a bidiyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.