Badakalar N1.5bn: Ministar Mata ta Maka Shugabar Kwamitin da ke Bincikenta Kotu

Badakalar N1.5bn: Ministar Mata ta Maka Shugabar Kwamitin da ke Bincikenta Kotu

  • Ministar ma'aikatar mata, Uju Kennedy Ohanenye ta musanta zargin da majalisar wakilai ke yi mata
  • Ana zargin ministar da badakalar N1.5bn, da sauran tuhume-tuhumen almubazzaranci karkashin jagorancin Kafilat Ogbara
  • A sanarwar da hadimin Misis Uju, Musa AbdulRahman ya fitar, ya ce sun dauki matakin shari'a a kan shugabar kwamitin binciken

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Ministar ma'aikatar mata, Uju Kennedy Ohanenye ta ce ba za ta zauna ana kokarin dora mata laifin handame kudin gwamnati ba. Ta ce yanzu haka ta dauki matakin shari'a, inda ta garzaya kotu domin a bi mata hakkinta.

Uju Kennedy
Ministar mata ta gurfanar da shugaban kwamitin da ke bincikenta a gaban kotu Hoto: Uju Kennedy Ohanenye
Asali: Facebook

A bayanin da ta wallafa a shafinta na Facebook, Uju Kennedy Ohanenye ta ce ta shigar da shugabar kwamitin da ke bincikenta, Kafilat Ogbara kara gaban kotu.

Kara karanta wannan

Zargin N33bn: Bayan kwana 1 a kurkuku, kotu ta ɗauki mataki kan Ministan Buhari

Minista Uju ta musanta zargin badakala

Ministar mata, Uju Kennedy Ohanenye ta musanta zargin da kwamitin majalisar wakilai ke yi mata na badakalar N1.5bn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sahara Reporters ta wallafa cewa kwamitin majalisar harkokin mata karkashin jagorancin Kafilat Ogbara ta zargi ministar da barnatar da kudin jama'a.

Me ake zargin minista da aikatawa?

Majalisar wakilai na zargin Ohanenye ta yi amfani da Naira Miliyan 20 wajen sayen auduga da kuma batar da Naira Miliyan 45 kan bikin sabuwar shekara.

Haka kuma ana zargin ta da kashe Naira Miliyan 1.5 wajen sayen man fetur domin zubawa a motoci da ma neman wasu kudade da yawansu ya kai N1.5bn kudin yan kwangila.

Amma a sanarwar da hadimin ministar, Musa AbdulRahman ya fitar ranar Alhamis, ya ce sai da aka bi doka kafin kashe dukkanin kudade a ma'aikatar.

Kara karanta wannan

Ana fafutukar bawa mata mukaman gwamnati, an gano minista ta kashe miliyoyi kan sayen auduga

Majalisa ta dakatar da ayyukan ma'aikatar mata

A wani labarin kun ji cewa majalisar wakilai ta dakatar da ayyuka a ma'aikatar mata bisa zargin almubazzarancin kudin gwamnati.

Majalisar ta kuma bukaci ministar ma'aikatar, Uju Kennedy Ohanenye ta gurfana a gabanta domin amsa tambayoyi kan shubuha da ake da shi kan ayyukanta

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.