Matasan Najeriya
Omoyele Sawore, ɗaya daga cikin masu jan ragamar shirya zanga zangar lumana da za a yi yau ya musanta raɗe-raɗin cewa an ɗage zanga zangar zuwa watan Oktoba.
Mai ba shugaban ƙaa shawara kan harkokin ɗalibai, Sunday Asefun ya ce suna zargin wasu masu ƙarfin juya gwamnati da ake ce ma Cabals da hannu a zanga zanga.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakile masu shirin gudanar da zanga-zanga a gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024 inda ta ce a filin wasa kawai za su tsaya.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gargadi matasa kan shiga zanga-zanga a Najeriya inda ya ce harkar da ba ta da tsari da kuma shugabanci kwata-kwata.
Babbar Kotun jihar Ogun ta umarci masu gudanar da zanga-zangar da su yi a wurare guda hudu kacal a jihar bayan shigar da korafi gabanta da gwamnati ta yi.
Karamin Ministan karafa a Najeriya, Uba Maigari ya roki 'yan jihar Taraba alfarma da su guji fita kan tituna domin gudanar da zanga-zanga da ake shirin yi.
Kungiyar NADECO a kasar Amurka ta gargadi gwamnatin Najeriya kan taba masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya. Ta ce Tinubu ma ya yi zanga zanga a baya.
Kungiyar Ja'oji da ke jihar Kano ta fito zanga-zanga domin nuna goyon bayan Shugaba Bola Tinubu inda ta kalubalanci masu fita gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.
Daya daga cikin jagororin zanga zanga a Najeriya Inibehe Effiong ya zargi yan sanda da kama matashi mai suna Okpe Kingsley Adegwu bayan ya fito zanga zanga a Legas.
Matasan Najeriya
Samu kari