Hankula Sun Tashi, Yan Sanda Sun Cafke Matashin da Ya Fito Zanga Zanga
- Lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Inibehe Effiong ya zargi rundunar yan sanda da cafke wani matashi mai wasan barkwanci
- Inibehe Effiong ya bayyana matakin gaggawa da shugabannin zanga zanga a Najeriya suka dauka bayan kama matashin da aka yi
- Hakan na zuwa ne bayan shugabannin zanga zangar a Najeriya sun yi zama da shugaban yan sanda na kasa kan ba su cikakkiyar kariya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Matasa masu shirin fita zanga zangar adawa da tsadar rayuwa sun fara fuskantar kalubale wajen yan sanda.
Daya daga cikin jagororin zanga zangar, Inibehe Effiong ya zargi rundunar yan sanda a jihar Legas da kama wani matashi.
Legit ta tatttaro abin da lauyan ya fada ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanene matashin da ake zargi an kama?
Inibehe Effiong ya zargi cewa yan sanda sun kama Okpe Kingsley Adegwu a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuli.
Rahotanni sun nuna cewa Okpe Kingsley Adegwu ya kasance mai wasan barkwanci a kafafen sada zumunta.
Zanga zanga: Dalilin kama matashin
Lauyan ya ce matashin ya fito zanga zanga ne kan yadda ake shan wahalar rayuwa a mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
An ruwaito cewa matashin yana rike da takarda da ya rubuta cewa yan Najeriya suna wahala sosai ya kamata Tinubu ya tausaya musu.
Halin da ake ciki bayan kama matashin
Har ila yau lauyan ya ce a yanzu haka matashin na kulle a ofishin rundunar yan sanda a jihar Legas tun ranar Lahadi.
Inibehe Effiong ya kara da cewa sun tura lauya zuwa hedikwatar yan sandan jihar Legas domin ganin matashin ya fito.
Zanga zanga: Yan sanda sun zauna da matasa
A wani rahoton, kun ji cewa yan sanda sun bukaci masu shirya zanga zangar adawa da tsadar rayuwa su bayyana sunayensu kafin samun izinin hukuma.
Wasu daga cikin jagororin a Najeriya sun ba rundunar yan sanda bayanansu kuma sun tattauna da rundunar a ranar Talata, 30 ga watan Yuli.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng